Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya yi kira ga kasar China ta yi taka tsantsan wurin ba wa Najeriya bashi.
Sanatan ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba yayin da ya ke magana wurin wani taro da Cibiyar Nazarin China (CCS) ta shirya a birnin tarayya Abuja.
Yayin da ya ke yaba wa China wurin kawo cigaba a Najeriya da Afirka baki daya, ya ce China ta rika bada bashi ne kawai wanda zai kawo sauyi a rayuwar yan Najeriya. Ya ce: “Yana da muhimmanci duk da kasarku na son tallafawa Najeriya wurin aiwatar da ayyukanta, a sani cewa wadanda ke gwamnati suna wurin ne na dan lokaci.
“Bashin da za a karbo a kasarku ya kasance mai muhimmanci, wanda zai kawo canji a tattalin arzikin kasar. “Za ku iya taimaka mana da bashi kuma kuna iya yin hakan ta hanyar wadanda suka zo wurin ku.
Shehu ya kuma yi kira ga jam’iyyar Communist ta gayyaci shugabannin jam’iyyun siyasar Najeriya zuwa taronta na gaba don su koyi yadda China ke amfani da jam’iyya don kawo cigaba a kasarsu.