Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya nada alkalai 11 na babbar kotun birnin tarayya Abuja.
Buhari ya aike sunayen alkalan zuwa majalisar dattawa domin tabbatar da su a bisa ga wata wasika wanda Shugaban majalisar dattawan, Ahmad Lawan ya karanto, a zamansu na yau Talata, 7 ga watan Yuli, jaridar Premium Times ta ruwaito.
Sabbin alkalan da aka nada sun hada da:
- Edward Okpe (Benue)
- B. Abubakar (Borno)
- M. Francis (Delta)
- Jude Nwabueze (Delta)
- Josephine Enobi (Edo)
- Christopher Opeyemi (Ekiti)
- Mohammed Idris (Kano)
- Hassan Maryam Aliyu (Kebbi)
- Fasola Akeem Adebowale (Lagos)
- Hamza Muazu (Niger)
- Abubakar Useni Musa (Adamawa)
A wata wasikar kuma, shugaban kasar ya bukaci tabbatar da sake nada Umar Danbatta a matsayin mataimakin shugaban hukumar sadarwa ta Najeriya wato NCC karo na biyu inda zai shafe shekaru biyar.
Buhari ya kuma nada jami’ai uku a matsayin mambobin Hukumar Kula da Dabi’u (CCB).
A wani labarin kuma, shugaba Muhammadu Buhari ya sabonta nadin jakadu 12.
Shugaba Buhari, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis ta hannun mai magana da yawun sa, Garba Shehu, ya ba ‘yan Najeriya tabbacin yin adalci yayin nadin wakilci da kuma dukkan abin da ya shafi shugabanci.
Shugaban kasar ya ba da tabbacin hakan ne biyo bayan korafin da aka yi kwanan nan bayan nadin sabbin jakadu 41 da ya yi, inda wasu jihohin kasar suka tashi fayau.
Shugaba Buhari, wanda ya sake taya jakadun murna sabunta mukaminsu, ya bukaci da su ci gaba da rike martaba da kuma inganta dabi’un shugabanci a Najeriya, yayin da suke rike kyakkyawar alaka da sauran kasashe.
Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, shugaba Buhari ya ayyana sunayen mutum 41 da zai nada a matsayin kananan jakadun Najeriya zuwa kashen ketare
Hakan na kunshe ne a wasikar da shugaba Buhari ya aike wa majalisar dattawa na neman amincewarta da mutanen da za su wakilci Najeriya a wasu kasashe na ketare.