Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, bakwai ga watan Safar shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyar ga watan Satumba shekarar 2020.
- Yau ma kamar jiya zan fara ne da batun wutar lantarki. Kamar shekaranjiya, jiya ma haka muka wayi gari ba wutar. Muka yini har muka kwana zuwa yanzun da asubah da nake wannan rubutu babu wutar. Ka ga da gaske gwamnati ta kara wa talakan Nijeriya kudin zama a duhu. Gwamnatin kuma ta masu gaskiya. Har talaka na korafin ina fa gaskiyar take a nan? Ba a ba ka wuta ba, wata ya kare an zo an maka kerere sai ka biya kudin zama a duhu kuma kudi tsugugu ai wannan fashi ne da kidinafin aljihun talaka da rana tsaka kata.
- An tashi baram-baran tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago a tattaunawarsu a kan karin kudin zama a duhu da kudin mai. A yanzun sai litinin za su kuma zama don ci gaba da tattaunawar.
- Kungiyoyin kwadago sun yi kira ga sauran bangarori da ke zamn kan su, a tafi yajin aiki da zanga-zanga ranar 28 ga watan nan don nuna rashin jin dadi da karin kudin zama a duhu da na mai da gwamnatin tarayya ta yi.
- Gwamnatin Tarayya ta ce za a gudanar da bikin cika shekara sittin da samun ‘yancin kan kasar nan, sai dai bikin ba zai yi wani armashin a zo a gani ba saboda halin da duniya ta shiga na kwaronabairos.
- Ibrahim Magu ya kalubalanci duk wani wanda ya san ya ba shi cin hanci ya karba, ya yi wa Allah Ya fito fili ya bayyana.
- Ministan Shari’a Malami ya ce kin zuwansa gaban kwamitin binciken Magu don ba da shaida bai saba wa tsarin mulkin kasar nan ba.
- Dakarun Lafiya Dole sun ce sun kashe wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram da mayakansu a Tafkin Cadi.
- Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba wuta. Ga tsadar taki ga ambaliya. Ga gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari idan sun zabe shi zai gyara. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Gas ya yi bindiga a Legas ya yi sanadiyyar konewar gidaje fiye da ashirin da uku, da ababen hawa goma sha hudu sai dai babu rai da ya salwanta.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi. Wasu malaman jami’a ma wata uku zuwa hudu ba albashi.
- A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito an jima da safe, akwai shafukana na labarun da na rubuta a wannan dandali daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis.
- Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 125 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 37
Filato 18
Abuja 17
Ogun 15
Ribas 10
Binuwai 7
Kaduna 7
Anambara 5
Oyo 3
Kuros Ribas 2
Ondo 2
Edo 1
Imo 1
Jimillar da suka harbu 57,849
Jimillar da suka warke 49,098
Jimillar da ke jinya 7,649
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,102
- Shugaban Amurka Donald Trump ya ce dole Majalisar Dinkin Duniya ta kama kasar Caina da laifin kirkiro da cutar kwaronabairos.
Mu wayi gari lafiya.
Af! Ta Mamman Shata. A gargadi mai gina ramin mugunta.
Za a iya leka rubutun yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2711993192406408&id=2356865571252507
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.