Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata goma sha daya ga watan Safar, shekarar1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da 29 ga watan Satumba na shekarar 2020.

  1. Shugaba Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani tsari na aiki da gaskiya wato National Ethics and Integrity Policy. Ana cikin kaddamarwar hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta gano wata naira biliyan biyu da rabi da ‘yan kai a boye a banki, kudin da aka ce an kashe su wajen ciyar da ‘yan makaranta a lokacin da ake kullen kwaronabairos.
  2. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika wa majalisar dokoki ta kasa kudirin dokar gyara ga bangaren man fetur Petroleum Industry Bill da za ta kafa wani kamfanin mai mai zaman kansa, da zai maye gurbin kamfanin mai na kasa NNPC da za a soke, da su hukumar kula da kayyade farashin mai PPPRA da sauransu.
  3. Kotu ta ci Sanata Elisha Abbo tarar naira miliyan hamsin saboda kama shi da laifin cin zarafin wata a wajen sayayya.
  4. Wasu rassan kungiyoyin kwadago irin su na jihar Edo, sun ce uwar kungiyar kwadago ta kasa ta ba su kunya da ta yi saurin dakatar da yajin aikin da aka kudurta farawa jiya.
  5. Gwamna Zulum na jihar Barno ya samu nasarar mayar da daruruwan mutanen Baga gida, bayan sun haura shekara biyu suna gudun hijira. Ya mayar da su gida cikin matakan tsaro, ya kuma raba musu kayan abinci da sutura da sauran muhimman kayayyakin da suke bukata.
  6. Mutanen Jibiya ta jihar Katsina, sun yi zanga-zanga har da banka wa ofishin ‘yan sanda wuta don nuna bacin ransu a kan matsalar tsaro. Suka yi zargin jami’an tsaro sun mayar da hankali ga tsaron kada a shigo da shinkafa fiye da tsaron rayukan talaka.
  7. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace, shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wuta, ga tsadar taki ga ambaliya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  8. Duk da gwamnati ta soke karin kudin zama a duhu, sai ga kamfanin karbar kudin zama a duhu, jiya ya shiga unguwanni yana yankar wayoyin wadanda ake bin bashin kudin zama a duhu.
  9. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida suna jiran ariyas na sabon albashi.
  10. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 136 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 71
Ribas 23
Filato 12
Adamawa 6
Oyo 6
Kaduna 6
Abiya 3
Abuja 3
Katsina 2
Kwara 2
Bauci 1
Barno 1
Edo 1

Jimillar da suka harbu 58,460
Jimillar da suka warke 49,895
Jimillar da ke jinya 7,454
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,111

Mu wayi gari lafiya.

Af! A cikin abubuwan da gwamnatin tarayya ta dau alkawari bayan janye karin kudin zama a duhu shekaranjiya, har da tallafa wa ma’aikatan gwamnati da abin da ake kira PARLIATIVE ina fata na rubuta haruffan kalmar daidai? Shi ne wasu ke tambayar gwamnatin tarayya. Ina ariyas da yawancin ma’aikatan gwamnati ke bi na sabon albashi kusan shekara daya da wata shida gwamnati ba ta biya su ba har yau?
Ina albashin wasu malaman jami’a da ke bin wata da watanni?
Ina batun sabon albashi da ya dade da zama doka da har yau ba a soma biyan yawancin ma’aikata ba? Ina alawus-alawus da yawancin ma’aikatan lafiya ke korafin suna bi? Ina tallafin da aka ce za a yi a lokacin kulle na kwaronabairos?
Ina?
Ina??
Ina???

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2715553688717025&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply