Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalama alaikum barkanmu da asubahin talata, ashirin da shida ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha biyar ga watan Satumba, shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 132 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 52
Gwambe 27
Filato 17
Kwara 10
Inugu 9
Ogun 9
Katsina 3
Ekiti 2
Bauci 1
Oshun 1
Ribas 1

Jimillar da suka harbu 56,388
Jimillar da suka warke 44,337
Jimillar da suke jinya 10,968
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,083

  1. Yau ma’aikatan lafiya za su shiga yini na biyu da soma yajin aikinsu na gargadi na kwana bakwai, da bayanai ke nuna tabbas yajin aikin nasu ya shafi majinyata da dama a asibitoci.
  2. Mailafiya ya amsa gayyatar hukumar DSS karo na uku inda ya bayana cewa a yanzun ya zama muryar al’uma musulmi da kirista da ba su da kafar fadin albarkacin bakinsu.
  3. Wasu manya kamar irin su tsohon shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Attahiru Jega, da Onaikan da sauransu, sun ce bugun ya yi wa talakan Nijeriya yawa wanne zai ji da shi? Suka ce ga kwarona, ga matsalar tsaro, ga karin kudin wuta da na mai, ga tsadar rayuwa, ga talauci.
  4. Kungiyar nan ta kare hakkin bil’Adama SERAP, ta kai Shugaban Majalisar Dattawa Lawan da na Majalisar Wakilai Gbajabiamila kotu a kan rashawa.
  5. Femi Falana ya garzaya kotu ya kai karar gwamnatin tarayya da ta jihar Kano kotu a kan hukuncin kisa da kotu ta yanke wa mawakin da ake zargin ya aibanta fiyayyen halitta.
  6. Manyan makarantu da ke jihar Kogi na haramar komawa makaranta, haka nan gwamnatin jihar Kano ta ba da umarnin bude kwalejojin kere-kere na jihar guda shida, sai jihar Legas da kungiyar malaman jami’a da ma’aikatan jami’a suka dode kofar shiga jami’ar Legas a kan sabon albashi da har yanzun ba su shaida ba.
  7. A jihar Kaduna bayanai ke nuna kidinafas na ci gaba da cin karensu ba babbaka a sassa daban-daban na jihar. Na baya-bayan nan su ne wata mata mai goyo, da wasu matan uku, da manoma goma sha daya da aka yi kidinafin, aka kuma harbi mutane da dama a yankin karamar hukumar Chikun.
  8. A jihar Nasarawa wasu kidinafas sun kashe jami’an hukumar kiyaye hadurra biyu, suka yi kidinafin wasu jami’an goma.
  9. Jami’an ‘yan sanda su dubu talatin da daya za a tura jihar Edo don tabbatar da tsaro a zaben gwamnan jihar da za a yi. Tuni ma Abdul Salam Abubakar ya je jihar tare da bukatar jam’iyyun siyasa na jihar, su sanya hannu a wata yarjejeniya ta zama lafiya.
  10. Zirga-zirgar jiragen sama ta kankama a nan cikin gida Nijeriya har ma da zuwa kasashen waje.
  11. Salami ya fatattaki lauyoyin Magu, su fita daga inda kwamitinsa ke zama.
  12. Gwamnatin Tarayya ta yunkura don tabbatar da ‘yan Nijeriya sun mayar da ababen hawansu sun koma masu aiki da man gas maimakon fetur da ke tsada.
  13. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wutar lantarki, ga tsadar taki ga ambaliya. Ga gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

15 A jihar Katsina wani jagoran ‘yan bindiga da ake kira Sada, ya ga uwar bari ya mika kansa ga sojoji.

  1. Wani lauya mai kare hakkin bil’Adama zai kai hukumar EFCC kara kotu, a kan yadda take kiran ‘yan jarida suna daukar hotuna da labaran wadanda suke zargi ko tuhuma ana watsa wa duniya, alhali zargi kawai take yi ba a kama mutum da laifi ba.
  2. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi. Wasu malaman na jami’a ma na bin albashin wata uku.

Kare da ya ga rawar kura ya ce da kyau.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Mu dai an kara mana kudin wuta, amma gaskiya kudin zama a duhu aka ninka mana. Misali jiya gabadaya ba mu da wuta sai cikin dare aka dawo da ita.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply