Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, biyar ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyar ga watan Agusta, na shekarar 2020.

  1. Yanzun karfe hudu da rabi da minti hudu na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwaronanairos su 321 a jihohi da alkalumma kamar haka:

Legas 98
Abuja 34
Kaduna 30
Nasarawa 25
Binuwai 21
Filato 17
Ribas 15
Adamawa 11
Ogun 11
Inugu 9
Edo 8
Delta 7
Ekiti 7
Gwambe 5
Ebonyi 4
Bayelsa 4
Kano 3
Ondo 3
Kuros Ribas 2
Imo 2
Kabbi 2
Neja 2
Abiya 1
Bauci 1

Jimillar da suka harbu 52,548
Jimillar da suka warke 39,257
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1004
Jimillar da ke jinya 12,287

Na ga wani bayani da ke cewa kafin alkaluman yau, Kaduna na da mutum 2000 da suka harbu da kwarona a cikjn alkaluma dubu hamsin da daya da ‘yan kai na kasar nan.

  1. Gwamnatin Tarayya ta soma debo ‘yan Nijeriya da ke kasar Sin wato Caina.
  2. Gwamnatin Tarayya za ta jinginar da wasu manyan tasoshin jiragen sama na kasar nan na tsawon shekara ashirin da biyar.
  3. Karfin tattalin arzikin kasar nan ya takura da kashi shida da ‘yan kai.
  4. Mailafiya ya ki amsa gayyatar da ‘yan sanda suka masa ya je shalkwatarsu jiya, ya garzaya kotu neman kare masa hakkinsa da ya ce ya ga alamu ana kokarin yi masa ballagaza da shi.
  5. Gobe laraba za a yi taron nan na kungiyar lauyoyi da suka gayyaci Malam Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, daga bisani kungiyar ta janye gayyatar sabida zargin El-Rufai na yin abubuwan da suke ganin sun saba wa akidar kungiyar, inda wani sashe na kungiyar ya ce in gaskiya ne a janye gayyatar da aka yi wa Obasanjo da Wike na Ribas su ma, saboda ba wanda ya fi Obasanjo da Wike hannun riga da akidojin kungiyar.
  6. Kungiyar fafutukar kafa kasar Biyafara IPOB ta kashe jami’an hukumar tsaro ta DSS su biyu a Inugu.
  7. Wani bayani na nuna a Arewa a cikin watanni bakwai, an kashe mutum dubu daya, da dari da ashirin da shida, aka yi kidinafin mutum dari uku da tamanin.
  8. Mutanen Katsina sun yi korafin jami’an hukumar kwastam na matsa musu da karbar na-goro.
  9. A jihar Katsina an yi kidinafin shugaban jam’iyyar APC da wasu mutum biyu.
  10. Kotu ta rufe ajiyar wasu kamfanoni goma sha biyu da ke bankuna sittin da biyar. Ba bankuna sittin da biyar aka rufe na wasu kamfanoni goma sha biyu kamar yadda na ji wani ya fassara a lokacin da yake karanta labaru a wani gidan rediyo da ke nan Kaduna jiya ba.
  11. Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar na uku ya kawo wa gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ziyara a kan matsalar tsaro ta kudancin jihar Kaduna.
  12. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zanta da wakilan Majalisar Dinkin Duniya a fadarsa, a kan matsalar tsaro da ta rashawa.
  13. A karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna, kidinafas sun yi kidinafin daliban wata makaranta da ke rubuta jarabawar WAEC tare da wasu mutanen kauye, da kashe mutum guda.
  14. Sojojin sama sun fara kula da marasa lafiya kyauta da rikicin kudancin jihar Kaduna ya shafa.
  15. Sojojin da suka kwace mulki a hannun Keita na kasar Mali sun ce sai sun dana mulkin kasar na shekara uku kafin su sauka. Kasashen yammacin Afirka sun yi niyyar fatattakar sojojin da karfin tuwo, sai suka lura ‘yan kasar na ta murnar kwace mulkin da sojoji suka yi, saboda haka suka tsahirta.
  16. Shugabannin matasan kasar nan na gudanar da wani gagarumin taro don ceto kasar nan daga cikin halin da take ciki.
  17. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata hudu ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi.
  18. Hukumar tara kudaden shiga ta tarayya FIRS ta tara naira tiriliyan daya da kusan rabi a watanni uku na baya-bayan nan, da suka dara wanda ta tara a watanni uku na farkon shekarar nan.
  19. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace, wata biyar ba wutar lantarki, ba hanya, ga gadar da sukan samu su haura ta balle, gadar da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi, zai gyara musu. Ga wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Gobe take ranar Hausa a duniya bakidaya 26/8/2020. Wacce hidima ka yi wa Hausar don ci gabanta da bunkasarta?

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2684990141773380&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply