Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalama alaikum barkanmu da asubahin Talata, daya ga watan Rabiul Sani,shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha bakwai ga watan Nuwamba, na shekarar 2020.

  1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 157 a jihohi da alkalulama kamar haka:

Legas 97
Oyo 37
Kaduna 9
Bayelsa 3
Edo 3
Ekiti 3
Ondo 2
Ogun 2
Filato 1

Jimillar da suka harbu 66,305
Jimillar da suka warke 61,162
Jimillar da ke jinya 3,980
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,162

  1. Kidinafas, da makasa da sauransu, na ci gaba da cin karensu ba babbaka a jihar Kaduna. Gwamnatin jihar Kaduna ta ce sojoji sun ce sun ceto mutum tara da Kidinafas da suka tare hanyar Kaduna zuwa Abuja suka yi kidinafin shekaranjiya. Sai dai kidinafas din sun kashe wani direba da fasinja. Mutum uku da kidinafas suka je kwalejin foliteknik ta Nuhu Bamalli da ke Zariya har suka harbi wani ne dai ba a ji inda suke ba. To a shekaranjiya da daddare wasu kidinafas sun auka Marabar Kajuru ta jihar Kaduna, suka kashe na kashewa, suka yi kidinafin na kidinafin. Sai jiya da rana tsaka kata. Wasu ‘yan bindiga, suka je wani kauye Albasu, da ke Sabon Birni a yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, suka kashe mutum goma, wata ruwayar ta ce mutum goma sha daya.
  2. Ministan Kwadago Ngige, ya ce har yanzun ba su gama gwada sahihanci da ingancin tsarin biyan albashin nan na UTAS da malaman jami’a suka kirkiri abin su, suka ce sun fi amince masa fiye da IPPIS da gwamnati ke kokarin kakaba musu, da suka ce tattare yake da kuskure da cutarwa gare su ba. Da ke nuna alamun babu ranar komawa makaranta ga daliban jami’a.
  3. Sabbin ‘yan sanda sun shaida wa BBC Hausa cewa, watansu shida ke nan ba albashi, da korafin saboda Allah in ba hanci suka ci ba, ya ake so su yi?
  4. Wasu masu zirga-zirga hanyar Kaduna zuwa Abuja, sun ce kwana bakwai a jere, kullum sai kidinafas sun tare hanyar da karfe bakwai zuwa takwas na safe, su yi dajin da mutane.
  5. Mutanen Zariya sun ce ba fa za su ci gaba da zura hajar mujiya kidinafas na cin karensu babu babbaka a ciki da wajen Zariya ba. Alhali ga su da makarantu na manyan sojoji da kanana a ciki da wajen Zariya, ya zama ga koshi ga kwanan yunwa.
  6. Hukumomin ‘yan sanda sun ce sun kama ‘yan sandan da suka kashe mutum biyu a Sharada ta jihar Kano, kisan da ya haddasa wata zanga-zanga, har kungiyar Aminasti ta yi tir da kisan.
  7. Mutane biyu ‘yan Nijeriya da ke kasuwanci a Ghana, suka yi barazanar za su kashe kansu da kansu saboda takaicin cin zarafin da ‘yan Ghana ke musu a can.
  8. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya, ya ki amincewa da takardun barin aiki da jami’an ‘yan sanda ke ta mikawa.
  9. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
  10. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na korafin da alamu sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa, bai gyara musu ba.
  11. Wani kamfanin na magunguna a Amurka ban da su Fzer, ya yi nasarar kirkiro rigakafin kwarona, da ya fi na su Fzer karfi. An yi gwajin maganin a mutum dubu talatin. Har yanzun ana matakin gwaji ne.
  12. Naira ta yi tuntsura gudigudi a kasuwar hadahadar kudade. Da a yanzun sai kana da Naira dari hudu da saba’in da biyar, za ka iya sayen Dala guda daya tal.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ya kamata dai Gwamna El-Rufai ya mike tsaye a kan matsalar tsaro. Don jihar Kaduna na neman zama tungar kidinafas yana ji yana gani.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=577365556399094&id=114506719351649

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply