Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Laraba, goma sha daya ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da 28 ga watan Oktoba, na shekarar 2020.

Af! A rana mai kamar ta yau 28 ga watan Oktoba na shekarar 2016 wato shekara hudu daidai, da karfe 6 da minti goma na bayan asubah, na yi wannan rubutun kamar haka:

‘Assalamu Alaikum Jama’a barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, kuma suna na Is’haq Idris Guibi. Juma’a biyu ba mu yi addu’a ba saboda haka yau kam addu’a za mu yi saboda muhimmancin wannan rana. Mu fara da yi wa Annabi Muhammad S.A.W salati, sannan mu ci gaba da yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari addu’ar nasara a yakin da yake yi da manyan gafiyoyin kasar nan, da ba shi ikon iyar da nufinsa, da kuma gyara a inda ya yi kuskure da ikon sanin makiyan talakawa da ke zagaye da shi Amin. Allah Ya jikan iyayenmu da kakanninmu da kakannin kakanninmu, wadanda iyayensu ke da rai Ya ba su tsawon kwana da lafiya da gamawa da su lafiya Amin. Wadanda iyayensu ba su da lafiya Allah Ya ba su lafiya. Allah Ya kare mu da iyalanmu marasa lafiya Allah Ya koro sauki. Allah Ya saukaka mana wahalhalun da muke ciki Ya yafe mana abubuwan da muka aikata ba daidai ba. Allah Allah Allah mun tuba.Allah Ka ba mu abinda za mu ci mu sha mu sanya da wajen kwana. Allah duk wanda yake cikin kunci Ka yaye masa. Duk wanda yake hannun miyagu Ka kubutar da shi. Allah Ka mana katangar karfe da duk wani mugu ko azzalumi ko maketaci ko mushiriki ko makiyi. Allah Ka kare mu daga tsautsayi da asara Ka biya wa kowa bukatunsa na alheri Amin. Jama’a mu yi juma’a lafiya’

To ga labarun na wannan asubahin kamar haka:

  1. Gwamnatin Tarayya ta ba da gobe Alhamis ta zama ranar hutu domin Maulidin waiwayowar ranar da aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W wato 12 ga watan Rabi’ul Awwal.
  2. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika wa Majalisar Dattawa sunan Farfesa Yakubu Mahmoud don ta amince wa shugaban kasan ya sake nada shi shugaban hukumar zabe wa’adi na biyu, sakamakon karewar wa’adinsa na farko.
  3. Miinistar Ayyukan Jinkai Sadiya Farouk, ta sanar da BBC cewa ita da shugaban kasa Buhari sun fita sal da sabulu a kan kayayyakin agaji na kwarona, da ta san sun raba wa gwamnoni su raba wa jama’a, gwamnoni suka ki rabawa.
  4. Iyalan mutanen nan 6 da ‘yan sanda suka kashe a Apo ta Abuja a shekarar 2005, sun sake tado da maganar a yanzun.
  5. Mutanen Abuja sun soma korafin dogayen layukan mai.
  6. A jihar Legas an kama mutane 520 da ake zargi da wasoson kaya, a Abuja ma sojoji sun damke wadanda suka je sansanin ‘yan bautar kasa da ke Kubwa, don wasoson kayayyakin da ke sansanin.
  7. Gwamnatin jihar Legas ta ba da umarnin bude dukkan kasuwanni da ke jihar.
  8. A jihar Adamawa masu wasoson kaya sun auka inda kwastam ke ajiye kaya, da sa wa hukumar kiyaye hadurra wuta. Nan ma an kama wasunsu.
  9. Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta ce za ta binciki daga ina kayayyakin da ake ta wasosonsu suka fito.
  10. Kawancen kungiyoyin da suka samar da tallafin da ake ta wasosonsu, ta ba matasan da ke wasoson hakuri, su tsahirta da wasoson haka nan.
  11. Idan Allah Ya kai mu watan Afriku na shekara mai zuwa, ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.
  12. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 51
Abuja 15
Filato 11
Kaduna 8
Oyo 8
Ribas 8
Ogun 4
Edo 2
Imo 2
Kwara 2
Delta 1
Kano 1

Jimillar da suka harbu 62,224
Jimillar da suka warke 57,916
Jimillar da ke jinya 3,173
Jimillar da suka riga mu gidan gaakiya 1,135

  1. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru wato tun zamanin ‘yan siyasa na PDP zuwa na APC sun bar su ba hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi, zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa, bai gyara musu ba.
  2. Ma’aikata sun soma korafin hantsi ya soma duban bakin ludayi. Wato yau 28 suna jiran dilin-dilin.

Yanzun karfe hudu da minti daya na asubah, ga ladanai can na ta rige-rigen kiran Assalatu.
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply