Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Lahadi takwas ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyar ga watan Oktoba na shekarar 2020.

  1. Yau ashirin da biyar ga wata ya kamata a soma jin dilin-dilin na watan nan daga yau.
  2. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu ya ce zanga-zangar da wawushe kayan mutane da na gwamnati, da lalata kayan mutane da na gwamnati, da far ma wasu mutane masu zaman kansu da jami’an gwamnati, da kashe jami’an tsaro da sauran jama’a haka nan ba sididi ba sadada ya isa haka nan kowa ya shiga taitayinsa. Saboda haka ya ba da umarni hanzarta baza ‘yan sanda ko’ina don sanya kafar wando guda da masu kunnen kashi.
  3. Ana ci gaba da wawar kayayyakin abinci a rumbuna da sito-sito na kayan abinci da sauransu da ke jihohi daban-daban na kasar nan musamman jihohin kudu da babban birnin tarayya da Jos da Kwara. Mu ma a nan jihar Kaduna an soma irin wannan yunkuri musamman a sassan karamar hukumar Chikun da Kaduna ta kudu, irin su Barnawa, da Kakuri, da Talabishan, da Marabar Rido, da Sabon Tasha, da Narayi, da Unguwar Romi, da har ya sa gwamnatin jihar Kaduna da farko ta sa dokar hana walwala a wadannan wurare ta sa’a ashirin da hudu, daga bisani gwamnatin ta ce dokar ta shafi dukkan ilahirin jihar Kaduna, domin kare dukiya da rayuka.
  4. A yanzun idan aka dauke wuta da karfe goma na dare, ba za a dawo da ita ba, sai karfe shida na safe. Kamar mu a jiya ma, da aka dawo da ita shida na safe, takwas na safe aka dauketa, ba a dawo da ita ba, sai wuraren karfe takwas na dare. Da aka dawo da ita ma, kyandir ya fi ta kumari. Zuwa goma na dare aka dauke. Sai kuma an jima da karfe shida su dawo da ita. Ga shi a yanzun duk yini naira dubu daya ne ko da wuta ko ba wuta, sai fa in mitarka ta iya-kudinka-iya-shagalinka ce. Sata da fashi da lantarki ba kunya ba tsoro.
  5. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  6. Idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, za su cika shekara biyu suna zaman dakon ariyas na sabon albashi.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Shekaranjiya Mohammed Isa Ashiru Kudan tsohon dan majalisar dokoki ta jihar Kaduna, kuma tsohon dan majalisar wakilai, kuma dan takaran gwamnan jihar Kaduna a zaben shekarar 2019 ya cika shekara 58 a duniya.
Ko shakka babu a lokacin da yake dan majalisa ta jiha zuwa ta tarayya ya kawo wa Kudan wadannan abubuwa:
A. Filayen wasa manya-manya
B. Cibiyoyin koyar da sana’o’i manya-manya
C. Makarantar horas da ‘yan sanda makekiya.
D. Rijiyoyin burtsatse maka-maka guda tamanin da ke aiki da hasken rana har guda tamanin (Solar)
E. Maka-makan hanyoyi sun haura goma
F. Maka-makan madatsun ruwa har guda bakwai
F. Maka-makan ajujuwa/azuzuwa goma-goma a kowacce makarantar firamare da sakandare.
G. Maka-makan cibiyoyin koyar da kwamfuta guda tara.
H. Babu wani aiki a kasar nan da bai saka dan Kudan a ciki ba.

Ka ga kuwa Isa Ashiru Kudan Ban Zazzau ba dan siyasa ne dan wala-wala ba.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a:

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2738756046396789&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply