Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin goma sha hudu ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da shida ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Gwamnatin jihar Kaduna ta yi kira ga al’umomin karamar hukumar Zangon Kataf da na karamar hukumar Kauru da ke fada da juna su yi hakuri su zauna lafiya.
  2. Sojojin sama sun ce a watan jiya na Yuni kadai, sun kashe ‘ya’yan kungiyar Boko Haram su saba’in da shida a Arewa Maso Gabashin Kasar nan.
  3. Ministar Ayyukan Jinkai Sadiya Faruk ta ce a yanzun haka akwai wadanda suka mallaki wuraren kasuwancinsu na kashin kansu su dubu dari da tara, da dari takwas da ashirin da uku, sakamakon tallafa musu da gwamnatin tarayya ta yi.
  4. Wasu malaman jami’o’i ban da wadanda rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan, akwai wadanda har yanzun ba su ga albashin watan jiya ba, kuma ashe su ma suna ta zaman jiran ariyas, kamar yadda ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya suka kwashe shekara daya da kusan wata uku suna dakon ariyas na sabon albashi, ba amo ba labari.
  5. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su dari biyar da arba’in da hudu a jihohi da alkaluma kamar haka :

Legas 199
Ebonyi 65
Oyo 46
Ogun 31
Edo 30
Abuja 28
Katsina 25
Filato 15
Bayelsa 11
Kaduna 10
Adamawa 10
Akwa Ibom 8
Gwambe 7
Kano 4
Taraba 3
Ribas 2
Abiya 2
Ekiti 1

Jamillar wadanda suka harbu mutum dubu ashirin da takwas, da dari bakwai da goma sha daya, wadanda suka warke, mutum dubu goma sha daya da dari shida da sittin da biyar, wadanda suka riga mu gidan gaskiya mutum dari shida da arba’in da biyar. Wadanda ke jinya mutum dubu goma sha shida, da dari hudu da daya.

A yi hakuri da yake karshen mako ne labarun kan yi karanci shi ya sa aka ga ba su da yawa.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Salim Is’haq Guibi na barar a sa shi a cikin addu’a ta kariya.

Af!! A rana mai kamar ta yau 6 ga watan Yuli na shekarar 2018 wato yau shekara biyu cur na saki wannan rubutu:

‘Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, ashirin da biyu ga watan Shawwal, shekara ta 1439 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da TALATIN DA SHIDA ga watan YUNI ga ire-irenmu da albashi shiru har yanzun, SHIDA ga watan YULI ga wadanda suka cinye albashin watan YUNI, shekarar 2018.

Yau korafe-korafen da jama’a suka turo mun ne zan lissafo har da wadanda na ji da kunnuwana.

Korafi na farko tun ma kafin ‘yan sandan kwantar da tarzoma su yi bore akwai dan sandan da ya turo mun sakon don Allah in taimaka in fadi kukan su a kan kudaden su da ke makalewa su da ke can yankin Maiduguri, sai sun aika gida ake aike musu da kudi.

Korafi na biyu da yake ina da dalibai mata da na koyar da ke auren sojoji manya da kanana, su ma sun yi mun korafin ana kin biyan sojoji hakkokknsu kuma ba su da wajen kai kara kuma ba damar yin bore irin na ‘yan sanda.

Sai korafi na uku, na wadanda suka gudanar da aikin zabe na kananan hukumomi na jihar Kaduna da har yanzun ba a biya yawancinsu kudadensu ba.

Sai korafi na hudu na sabbin malaman makaranta na jihar Kaduna da suka ce tunda aka dauke su aiki har yau wata hudu ke nan ba albashi.

Sai korafi na biyar, da dogarai da sauran ma’aikatan Hakimai na jihar Kaduna da aka soke musamman na Masarautar Zazzau, da ma wadanda ba a dakatar din ba, wata goma sha biyar ke nan ba a biya su ba, kuma babu takardar sallama.

Korafi na shida, jiya da yake na leka jami’armu ta Ahmadu Bello da ke Samarun Zariya, na shigo daya daga cikin bas-bas din da ke debo fasinja daga kofar ABU zuwa Kaduna, na ji dalibai na ta korafin kudin motar da suke karba a yanzun naira dari hudu zuwa Kaduna ya yi tsada. Ko ni na tuna bai dade ba nake biyan naira dari uku. Suka mayar da shi dari uku da hamsin. To yanzun suna karbar naira dari hudu.

Sai korafi na karshe da masu cin kasuwar Makarfi ta duk laraba, suka ce daga Danguzuri zuwa kasuwar akwai shingen ‘yan sanda uku, kowanne shinge sai direba da mai kaya sun ba ‘yan sanda cin-hanci kafin su kyale su su wuce.

Af! Na dawo da na shiga Jami’ar na ji suna ta korafin ba a biya su albashin watan yuni ba’

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Exit mobile version