Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, ashirin da takwas ga watan Safar, shekerar 1442 bayan hijirar cikamakakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha shida ga watan Oktoba, na 2020.
- Gwamnatin Tarayya da kungiyar malaman jami’a ASUU, sun tashi taron da suka yi jiya baram-baram ba su daidaita ba, amma za su ci gaba da tattaunawar mako mai zuwa.
- Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa ta gudanar da tata zanga-zangar ta lumana a kan matsalar tsaro a jihohin Arewa. Sai dai gamayyar ta yi zargin gwamnatin jihar Kano ta sa ‘yan daba sun tarwatsa mata zanga-zangarta a Kano har da far musu.
- Shugaban Kungiyar Gwamnonin jihohin Arewa Simon Lalong, ya ce suna goyon bayan #ENDSARS sai dai ya ce bai kamata ido ya rufe a yi watsi da alherin da ke tattare da SARS ba.
- Gwamnatin Tarayya ta ce za ta bude sansanonin horas da ‘yan bautar kasa da ke fadin kasar nan ranar goma ga watan gobe.
- Gwamnatin Tarayya ta nemi a hukunta wadanda suka kashe dan Nijeriya ta hanyar cinna masa wuta har ya kone a kasar Libiya.
- Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa INEC Farfesa Mahmud ya ce yau saura kwana 854 a gudanar da zabukan shekarar 2023. Hukumar ta kuma ce a ranar 18 ga watan Fabrairu na shekarar 2023 za a gudanar da zaben shugaban kasa.
- Sojojin sama na Nijeriya sun jefa bama-bamai sansanonin ‘yan bindiga da ke Ali-Kere a jihar Katsina.
- Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu gadar ba.
- A nemi jaridar Leadership Hausa da za ta fito an jima da safe, don karanta shafukana, da ke dauke da labarun da na kawo muku a dandalina, daga Juma’ar da ta gabata zuwa jiya Alhamis.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wajen wata takwas ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
- Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 148 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 66
Abuja 25
Oyo 13
Filato 11
Kaduna 7
Ribas 6
Ebonyi 5
Ekiti 4
Ogun 4
Imo 2
Ondo 2
Edo 1
Nasarawa 1
Taraba 1
Jimillar da suka harbu 60,982
Jimillar da suka warke 52,194
Jimillar da ke jinya 7,672
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,116
Mu wayi gari lafiya.
Af:
Jiya na ga wani rubutu da Dafta Aliyu Ammani ya yi a fesbuk, da nake ganin yana da kyau in kwafo muku shi sai dai cikin harshen Ingilishi ya yi shi kamar haka:
A Dangerous Signal
I heard the news first on VOAHausa. That after series of attacks on their communities by bandits, the poor people, disappointed by the inability of the police to protect them, raid the local police station and helped themselves with firearms from the armory, hoping to use the weapons in defending themselves against the bandits. The sad event happened in Kagara, Niger State.
This is a dangerous signal. Very dangerous signal!
The police is the symbol of government authority over its citizens. If the citizens of a country, both criminals and law abiding, started feeling the need to own guns, and are not only beginning to see in police formations sources of illegal firearms, but are also becoming courageous enough to attack such formations to grab weapons, then anarchy is staring us in the face.
When you ignore small things, small things become big things. Before you know it, Frankenstein monsters are born!
All hands, starting with the hands of those in power, must be on deck to tackle the security challenges that are gradually becoming the new normal in this part of the country.
Aliyu Ammani
U/Shanu Kaduna
15/10/20
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=554724235329893&id=114506719351649
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.