Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barknu da asubahin Alhamis, ashirin da bakwai ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha biyar ga watan Oktoba, shekarar 2020.

  1. Yau ake sa ran shugabanni kungiyar malaman jami’a ta kasa ASUU, za ta tattauna da gwamnatin tarayya, tattaunawar da ake sa ran suna kammalata malaman za su janye yajin aikin da suke kan yi.
  2. Yau gamayyar kungiyoyin matasan Arewa za ta wayi gari da zanga-zanga ta lumana shigen ta #ENDSARS a kan matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa a jihohin Arewa.
  3. A wasu jihohi an yi dauki-ba-dadi tsakanin masu zanga-zangar neman kawo sauyi ga aikin ‘yan sanda da kuma #ENDSARS, da masu adawa da wannan gwagwarmayar, inda aka ce masu adawa da gwagwarmayar sun kwashi kashinsu a hannu har wasu sun sheka barza’u.
  4. Za a koma makaranta a jihar Kaduna daga ranar goma sha takwas ga watan nan na Oktoba da muke ciki. Makarantu na firamare da na sakandare za su koma.
  5. Majalisar Wakilai ta yi nisa a muhawarar amincewa da kasafin kudi na 2021.
  6. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzu, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayyya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata bakwai ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
  8. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 179 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 116
Anambara 20
Abuja 9
Oyo 9
Ribas 9
Delta 3
Nasarawa 3
Edo 2
Kaduna 2
Ogun 2
Filato 2
Ekiti 1
Oshun 1

Jimillar da suka harbu 60,834
Jimillar da suka warke 52,143
Jimillar da ke jinya 7,575
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,116

Mu wayi gari lafiya.

Af!
a) Kwarona sai su jihar Kaduna ba ruwan su jihar Kano da su Kogi ko Kuros Ribas.

b) Jinjinata ta musamman ga malaman jami’a ASUU. Ka ga inda ake gwagwarmaya ba tsoro, ba gudu, ba ja da baya. Ka hada da su wa’a matsorata?

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Exit mobile version