Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Gui?i

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, ashirin da biyar ga watan Safar, na shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhamad S.A.W. Daidai da goma sha uku ga watan Oktoba, na shekarar 2020.

  1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 164 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 64
Abuja 26
Inugu 20
Kaduna 11
Oyo 11
Filato 8
Ondo 7
Anambara 4
Nasarawa 4
Oshun 3
Ebonyi 2
Imo 2
Binuwai 1
Ogun 1

Jimillar da suka harbu 60,430
Jimillar da suka warke 51,943
Jimillar da ke jinya 7,372
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,115

  1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bai wa Okonjo Iweala tabbacin goyon bayansa har sai ta kai ga madafin iko na hukumar hada-hadar kasuwanci ta duniya WTO, da idan ta yi nasara za ta zama bakar fata ta farko kuma mace da za ta dare kujerar shugabancin hukumar.
  2. A lokacin da masu zanga-zangar ganin an kawo karshen cin zarafin da ‘yan sanda ke yi wa jama’a ke ci gaba da zanga-zangar a manyan birane irin su Legas, wasu kuma ke tasu zanga-zangar ta kada a rushe rundunar SARS, Shugaban Kasa Buhari da Mataimakinsa Osinbanjo sun ba da tabbacin za a yi wa bangaren aikin ‘yan sanda gyara.
  3. Dakatar da karin kudin wuta da aka yi da mako biyu, ta kare, an kara mako guda domin kammala yadda za a sayar da wutar tsakanin gwamnati da ‘yan kwadago.
  4. A Abuja makarantun firamare da na sakandare sun koma makaranta jiya. Haka nan a ranar 26 ga watan nan za a bude manyan makarantu mallakar gwamnatin jihar Kano.

6 An tsige Shugaban Majalisar Dokoki ta jihar Edo Francis Okoye, an maye gurbinsa da wani.

  1. A wuraren Kuje da ke Abuja kidinafas sun yi kidinafin wajen mutum 18. Can kuwa a yankin Ikara ta jihar Kaduna wasu ‘yan bindiga ne suka kashe wani maigari, Musa Abubakar da suka fada masa gaskiya an aike su su kashe shi ne, suka kuma kashe shin.
  2. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan, ta jihar Kaduna sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yazun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba
  3. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafi shekara daya da wata bakwai suna dakon ariyas na sabon albashi. Kodayake na hango wani bayani da ke cewa shugabannin majalisar dattawa da na malaman jami’a sun yi ganawa ta sirri jiya wato sun sa labule.

Yanzun karfe hudu na asubah.
Mu wayi gari lafiya.

Af!

a) Iyayen yara na ta kirana a waya suna tambayata yaushe Gwamna El-Rufai zai bude makarantu yara su koma ne?

b) Mu dauka hadarin da ake zargin kasteliya sun haddasa har tifa ta buge keke-nafef mutun hudu suka mutu a ciki, a mahadar matatar mai ta Kaduna, a jihar Legas ko Ogun ko Oshun ko Ekiti ko Oyo ko Legas ko ma a nan kusa jihar Binuwai ko Anaca al-amarin ya auku me ake jin zai faru?

C) Mu dauka kisan mutanen Kidandan da ke yankin karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, a jihohin yarbawa ko inyamurai ko ma nan jihar Filato ko Binuwai aka yi kisan me muke jin zai faru?

d) Ko mun san saboda jihohinsu na can ne suka yi tsayin daka a kan #ENDSARS ya sa aka rusheta?

e) Ko mun san da ministan ilimi Adamu Adamu ya ce ba za a yi WAEC ba, jihohi shida na yankin yarbawa ne suka ce ba su yarda ba, dole kuma aka yi jarabawar?

f) Ina mutanen Jibiya ta jihar Katsina da suka yi zanga-zanga a kan matsalar tsaro aka kama su? In Oyo ko Oshun ko Ekiti ko Ogun ko Legas ne wani ya isa ya kama su?

Na yi nan.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://www.facebook.com/2356865571252507/posts/2727700520835675/

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Related posts

Leave a Comment