Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Litinin, ashirin da hudu ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha biyu ga watan Oktioba na shekarar 2020.

  1. Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta sanar da cewa gwamnan jihar Ondo Akeredolu na jam’iyyar APC shi ne ya lashe zaben gwmna na jihar da aka yi shekaranjiya Asabar da kuri’a dubu dari biyu, da casa’in da biyu, da guda dari takwas da talatin. Sai Jegede na PDP da ke da kuri’a dubu dari da casa’in da biyar, da dari bakwai da casa’in da daya.
    Har ma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya Akeredolu murna, da yaba wa hukumar zabe. Haka nan su ma ‘yan kallon zaben sun yaba wa shugaban kasa da hukumar zabe.
  2. Sakamakon zanga-zangar lumana da matasan kasar nan suka yi a ciki da wajen kasar nan, ta neman sai an rushe runduna ta musamman ta ‘yan sanda da ke yaki da ‘yan fashi, saboda zargin tana cin zarafin wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, shugaban ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, ya sanar da rushe sashen rundunar. Sai dai masu zanga-zangar sun ce ba su gamsu da rusheta ba, sai sun ga an kama manyansu da kananansu da ake zargi da cin zarafin jama’a an hukunta su. Shi kansa Shugaban Majalisar Wakilai Femi ya yaba wa Shugaban Kasa da Shugaban ‘Yan sanda saboda wannan mataki da suka dauka na share wa jama’a hawaye. A shekarar 1992 aka kirkiro wannan sashe don yaki da fashi da makami, a karshe ake ta kuka da shi.
  3. ‘Yan bindiga sun kashe mutane da dama a Kidandan da Kadai duk da ke yankin karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna. An ce jami’an tsaro da suka ji hare-haren sun tsananta da kazanta, sun kai dauki ta sama da kasa.
  4. Bayanai na nuna Gwamna Ganduje na jihar Kano ya dakatar da wani daga cikin hadiman gwamnatinsa saboda kalaman da ya yi a kan shugaban kasa Buhari, da ba su yi wa Ganduje dadi ba.
  5. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 163 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 113
Kaduna 21
Oshun 8
Ondo 5
Oyo 5
Ogun 3
Bayelsa 2
Taraba 2
Edo 1
Abuja 1
Katsina 1
Filato 1

Jimillar da suka harbu 60,266
Jimillar da suka warke 51,735
Jimillar da ke jinya 7,416
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,115

  1. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  2. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata bakwai ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi. Sai dai wasu bayanai na cewa gaskiya kudin biya ne gwamnati ba ta da shi. Don albashi ma da kyar take iya biya.
  3. Ana ci gaba da ankarar da masu shiga Kinkinau bayan karfe goma na dare, su dinga kaffa-kaffa don akwai barayin waya da na babur a hanyoyin shiga unguwar.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Yau Litinin ma’aikata za a koma aiki bayan hutun karshen mako. To mu dage da addu’a Allah Ya ci gaba da kare mu daga sharrin abokan aiki. Kuna aiki da mutane a ofis daya, ko ma’aikata daya ana washe maka baki da bude maka hakora kamar ana sonka, nan kuwa a zahiri ana cin dunduniyarka. Ko a maka sharri ko kazafi. Allah Ka mana maganinsu a duk inda suke Amin. Yanzun karfe hudu da minti bakwai na asubah ladan ya gama kiran assalatu.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply