Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, ashirin da biyu ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma ga watan Oktoba, shekarar 2020 wato 10/10/2020.

  1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronanairos 151 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 71
Ogun 26
Kaduna 17
Oshun 10
Oyo 8
Abuja 6
Ribas 6
Filato 5
Akwa Ibom 1
Ekiti 1

Jimillar da suka harbu 59,992
Jimillar da suka warke 51,614
Jimillar da ke jinya 7,265
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,113

  1. Yau za a wayi gari al’umar jihar Ondo za su rumfunan zabe don kada kuri’ar zaben gwamna na jihar. Tuni shugaban ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu ya ba da umarnin takaita zirga-zirga a jihar, daga karfe goma sha biyu saura minti daya na jiya da daddare, zuwa karfe shida na yammacin yau.
  2. Wata kungiyar sa ido a kan zaben na jihar Ondo da ke da kungiyoyin farar hula har guda dari hudu a cikinta TMG a takaice, ta soki yadda gwamnoni kasar nan suka yi tururuwa, tare da yin cincirindo a jihar Ondo da za a yi zaben gwamna na jihar a yau. Kungiyar ta ce an yi godo da gwamnonin su bar jihar sun ki, da ke nuna sun je murdiyyar zabe ne.
  3. Kungiyoyin matasa na ci gaba da gudanar da zanga-zanga a jihohin kasar nan ta neman sai an kawo karshen cin zarafin da ‘yan sandan da ke yaki da fashi da makami FSARS ke yi wa jama’a. Shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban ‘yan sandan Nijeriya, na ta ba matasan da ke zanga-zangar hakuri da tabbacin za a kawo karshen cin zarafin.
  4. Wani labari da na tsinkayo a fesbuk jiya na cewa ‘yan bindiga sun auka kauyen ‘Yan Kara da ke jihar Katsina jiya da yamma.
  5. Ana ci gaba da yin kira ga gwamnatin jihar Kaduna ta yi wa Allah ta bude makarantu yara su koma makaranta tunda jihohi na ta bude makarantu, na gwamnati da masu zaman kansu.
  6. Wasu bayanai na nuna tsarin IPPIS ya talauce ba kudi, shi ya sa har yau wadanda suka amince masa suka shigesa, yawancinsu bai iya biyansu albashin watan jiya ba, ga shi yau goma ga wata.
  7. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, suna can suna ci gaba da kasancewa a killace da alamu sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’dinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  8. Ma’aikatan jami’o’i manyansu da kanana, da malaman jami’o’i da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya suna yajin aiki. Wadanda suka yi saura na kwalejojin foliteknik na shirin zuwa yajin aiki su ma. Duk a kan IPPIS.
  9. Shekara daya da wata bakwai ke nan ma’aikatan kwalejojin foliteknik na gwamnatin tarayya, da jami’o’i da kwalejojin ilimi na dakon ariyas na sabon albashi.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ba bakon abu ba ne mu da ke zirga-zirga da ababen hawa a cikin garin Kaduna da Zariya, ka ga in ka kusa da inda ‘yan kasteliya suka sa shinge, ka ga sun tsaya tsakiyar titi suna tsayar da ku na gaba-gaba, da nufin sun hango wani da suke so, su tare da ke can bayanku. Wato tsayar da ku da suka yi, kun taimaka musu kama na bayanku. To an yi zargin abin da suka yi ke nan jiya a mahadar matatar mai ta kasa da ke can gaban Sabon Tasha. Sun hango mai tifar yashi, to akwai mai keke-nafef a gabansa, suka tsayar da nafef din don jin dadin tare mai tifa, aka ce shi kuma mai tifa ba birki, ya auka kan nafef, take a nan mutane hudu da ke cikin nafef suka mutu har da mai goyo.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2725293084409752&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta