Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalama alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, ashirin da daya ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da tara ga watan Oktoba, na shekarar 2020.

  1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 103 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 39
Ribas 21
Abuja 19
Oyo 6
Kaduna 4
Bauci 3
Ogun 3
Imo 3
Kano 2
Binuwai 1
Edo 1
Nasrawa 1
Filato 1

Jimillar da suka harbu 59,841
Jimillar da suka warke, 51,551
Jimillar da ke jinya 7,177
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,113

  1. A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito an jima da safe, don karanta labarun da na kawo daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis, a shafukana da ke jaridar.
  2. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da daftarin kasafin kudi na shekarar 2021 jiya, a gaban zaman hadin gwiwa na majalisar dattawa da ta wakilai. Kasafi ne na naira tiriliyan goma sha uku da ‘yan kai. Ya umarci ministoci da shugabannin ma’aikatu da hukumomi na gwamnati su je da kansu ba sako ba, don kare muradunsu a gaban kwamitocin majalisun. Ita kuma majalisar wakilai ta ce a makon gobe za ta soma muhawara a kan kasafin.
  3. Matasa na nan suna ci gaba da boren sai an kawo karshen cin zarafin da ‘yan sandan FSARS ke yi wa jama’a a kasar nan.
  4. A jiya hukumar zabe ta kasa ta raba muhimman kayayyakin zaben gwamna na jihar Ondo da za a yi gobe asabar idan Allah Ya kai mu.
  5. Shugabn Kasa ya ce sai fa dukkan ma’aikata sun shiga tsarin IPPIS in ma’aikaci bai shiga ba, ba shi ba albashi. Tsarin na IPPIS shi ya hada fada tsakanin malaman jami’a da gwamnatin tarayya, su kuma kwalejojin ilimi da na foliteknik da suka yarda suka shiga tsarin suke ta wayyo Allah tsarin ba dadi.
  6. Ngozi Okonjo Iweala ta kai mataki na karshe a fafatawar kai wa ga kujerar shugabancin WTO babbar hukumar kasuwanci da cinikaiya ta duniya.
  7. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba..
  8. Malaman kwalejojin foliteknik sun shirya tsab don soma yajin aiki, kamar yadda takwarorin aikinsu na jami’a, da na kwalejojin ilimi suka dade suna ciki, saboda tsarin nan na IPPIS da suka ce su da suka yarda suka shiga ba karamar kudarsu suke dandanawa ba. Ga baba Buhari ya ce dole sai kowa ya shiga.
  9. Shekara daya da wata bakwai ma’aikatan kwalejojin foliteknik na ci gaba da korafin ba ariyas na sabon albashi.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Yau juma’a mu dage da addu’ar Allah Ya mana maganin masharranta Amin. Kana zamanka mutum ya zauna ya maka sharri saboda bakin cikin ka fi shi.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=550159919119658&id=114506719351649

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply