Sharhin Bayan Labarai – Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, ashirin ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijiirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da takwas ga watan Oktoba na 2020.

  1. Jiya labarin da ya fi daukar hankalin jama’a shi ne nadin da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi wa Magajin Gari Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na goma sha tara, kuma bamalle na farko bayan mallawa sun shekara dari rabonsu da mulkin kasar Zazzau. Wadanda ya kara da su, da shugaban kasa Muhammadu Buhari, da Ahmed Tinubu duk sun taya shi murna.
  2. Yau Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin shekarar dubu biyu da ashirin da daya a gaban zaman hadin gwiwa na majalisar dattawa da ta wakilai da wuraren karfe goma sha daya na safiyar nan.
  3. Hankali na ci gaba da karkata ga rundunar ‘yan sandan nan ta musamman da ke yaki da masu fashi da makani F-SARS, inda shi kansa shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya ba da umarnin damke duk dan sandan da aka ga yana cin zarafin jama’a. Majalisar Dattawa ma ta kaddamar da bincike a kan hallayar ‘yan sanda da suka sabawa hankali. Haka nan Majalisar Wakilai ta ba shugaban ‘yan sanda makwanni ya hukunta ‘yan sandan da ake tuhuma da cin zarafin jama’a.
  4. Hukumomin sojan sama na Nijeriya sun kawo jiragen sama na yaki, da dakaru dazuzzukan jihar Kaduna da na jihar Zamfara don sanya kafar wando guda da kidinafas, da ‘yan bindiga da sauran miyagun mutane da ke boye a wuraren. Shugaban mayakan sama na Nijeriya ya ba sojojin umarnin su ci gaba da kai farmaki dajin babu kama hannun yaro.
  5. Malaman kwalejojin foliteknik sun ba gwamnatin tarayya wa’adin mako uku, ko ta yi wani abu a kan tsarin nan nata na IPPIS da ake ta korafi a kai ko su tsunduma yajin aiki. Tuni dai malaman jami’a, da na kwalejojin ilimi, da sauran ma’aikata kanana da manya na jami’o’i suka dukufa yajin aiki a kan tsarin na IPPIS.
  6. Gwamnoni goma sha bakwai suka ruga jihar Ondo da jibi asabar za a yi zaben gwamnan jihar.
  7. Jami’an kwastam sun kama wani mutum a tashar jiragen sama ta Kano, za shi Dubai, boye da ATM/Eti’yam guda 5,342 a cikin wake.
  8. Wasu ‘yan majalisar wakilai su biyu ‘yan PDP sun sauya sheka zuwa APC.
  9. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace, shekara da shekaru ba hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzu, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har yana shirin gama wa’adinsa bai gyara musu ba.
  10. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 155 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 84
Ribas 31
Kaduna 12
Oshun 10
Abuja 7
Oyo 6
Ogun 3
Kwara 2

Jimillar da suka harbu 59,738
Jimillar da suka warke 51,403
Jimillar da ke jinya 7,222
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,113

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ga Af din rubutuna na ranar 28 ga watan jiya wato 28/9/2020 da na yi AF a kan Magajin Garin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli :

‘Af! A lokacin da ake ci gaba da dakon Gwamna El-Rufai ya zabi sabon sarkin Zazzau, na lura rabon Mallawa da sarautar Zazzau shekara dari ke nan. Barebari sun yi mulki sau uku, Katsinawa sun yi sau biyu, sai kuma a dan kyale Mallawa su hau. Amma fa ra’ayina ne in kuma akwai mai sayen ra’ayin sai mu yi jinga. Ni mahaifina asalinsa bakano ne, mahaifiyata asalinta Katsina gidan sarautar Katsina, suka haife ni a kasar Zazzau. Ka ga idan zan yi son kai ne sai in ce a sake bar wa Katsinawa su yi mulki karo na uku. Amma a bar wa Mallawa. A tuna mun sunan bamallen ma? Af! Sunansa Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli Magajin Garin Zazzau.

Na yi nan’

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply