Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, goma sha tara ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da bakwai ga watan Oktoba, shekarar 2020.
1 Gobe alhamis idan Allah Ya kai mu da wuraren karfe goma sha daya na safe, shugaban kasa Buhari zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2021 naira tiriliyan goma sha uku da ‘yan kai 13.09 trillion naira. Zai gabatar ne a gaban zaman hadin gwiwa na majalisar dattawa da majalisar wakilai.
- ‘Yan sanda dubu talatin da uku aka kai jihar Ondo saboda zaben gwamna na jihar da za a yi ranar asabar mai zuwa.
- Bangarorin da za su fafata a zaben gwamnan jihar Ondo, sun sa hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya ta su Janar Abdulsalam da Mathew Kukah, da Sarkin Musulmi ya halarta.
- Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum shida a karamar hukumar Riyom ta jihar Filato, har da wani dan sarki Changyan.
- Dakaru sun yi maganin wasu barayin shanu da ke addabar jihar Katsina da ta Zamfara har suka ceto wata da suka yi kidinafin.
- Kidinafas sun sako wata mata da suka yi kidinafin a Kasuwar Magani ta jihar Kaduna bayan an ba su naira miliyan biyar da babur sabo.
- Kamfanin da ke nemo wutar lantarki, ya zargi kamfanin da ke dakon lantarkin, da kamfanonin da ke raba wa jama’a lantarkin da laifin kin kwaso lantarki megawat 4000 da kamfanin ke nemowa a kullum don a ba jama’a, da ya sanya ake asarar wutar, maimakon a ba jama’a. Wato ga lantarkin ba a ba jama’a an bari yana tafiya a banza ana asararsa, talaka na biyan kudin wutar da ba a ba shi ba.
- Dukkan makarantu na gwamnati da masu zaman kansu da ke jihar Katsina sun koma makaranta. Jihar Sakkwato ma za ta bude dukkan makarantu ranar goma sha daya ga watan nan.
- Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas ya haramta wa jami’an FSARS da ke yaki da ‘yan fashi, tsare duk wani da suke tuhuma.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i na ci gaba da korafin shekara daya da wata bakwai ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi. Ga albashin watan Satumba har yau bakwai ga watan Oktoba ba amo ba labari. Ga malaman jami’a, da sauran ma’aikata, da na kwalejojin ilimi duk kowa yana yajin aiki.
- Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can a killace ba hanya, gadar da sukan samu su haura ta karye, da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Kungiyar ECOWAS ta dage takunkumin da ta sanya wa kasar Mali bayan wadanda suka kifar da gwamnatin kasar sun sanar da sabuwar gwamnati ta rikon kwarya.
- Donald Trump na Amurka ya koma fadar White House bayan kwana uku a asibiti sakamakon harbuwa da kwaronabairos.
- Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 118 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 41
Ribas 19
Oshun 17
Nasarawa 13
Kaduna 5
Anambara 5
Edo 3
Ogun 3
Kwara 3
Ondo 3
Katsina 2
Neja 2
Filato 2
Akwa Ibom 1
Jimillar da suka harbu 59,583
Jimillar da suka warke 51,308
Jimillar da ke jinya 7,162
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,113
Mu wayi gari lafiya.
Af! Wani na ji yana cewa ya lura kidinafas da ke addabar mutanen jihar Kaduna, in sun je kidinafin, har da babura suke kidinafin. Ko in sun yi kidinafin ciniki ya kaya, sai su ce in za a kai musu kudin a hada musu da babur sabo. Wasu daga cikin wadanda aka yi cinikinsu suka dawo gida, na ba da labarin suna ta tara baburan waje guda, da alamu jira suke yi ruwan sama ya dauke, su dinga gungu suna kai hari kauyukan jihar Kaduna ko kisan kare dangi ko jidar jama’a zuwa daji wato kidinafin.
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
https://www.facebook.com/2356865571252507/posts/2722783121327415/
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya