Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalama alaikum barkanu da asubahin litinin, goma sha bakwai ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S..A.W. Daidai da biyar ga watan Oktoba na sbekarar 2020.

  1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 58 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Filato 18
Legas 15
Katsina 10
Ogun 5
Kaduna 4
Edo. 3
Ekiti 1
Abuja 1
Ondo 1

Jimillar da suka harbu 59,347
Jimillar da suka warke 50,268
Jimillar da ke jinya 7,466
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,113

  1. An sanar da ni daga Guibi cewa wutar lantarki da ke cikin abubuwan da nake ta korafi a kai ta soma samuwa. Saura hanya da gadar da Jaja, shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Suka zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  2. Mu ma dai rabonmu da wutar lantarki tun jiya da safe. Haka muka yini, muka kwana har zuwa yanzun karfe uku da rabi da wasu mintoci da nake wannan rubutu ba wutar. Talaka zai ci gaba da biyan kudin zama a duhu ke nan a kasata Nijeriya.
  3. Yawancin ma’aikatan gwamnatin tarayya musamman na bangaren ilimi har yau watan Satumba bai kare musu ba ballanta su shiga Oktoba. Yau 35 ga watan Satumba. Babu albashi babu dalilinsa. Wasu malaman jami’a na watan Mayu, wasu Yuni wasu Yuli. Wasu na Agusta.
  4. Litinin din nan ake sa ran ma’aikatan jami’o’i manyan da kanana su wayi gari da yajin aiki na gargadi na mako biyu.
  5. Malaman kwalejojin ilimi na ci gaba da yajin aiki.
  6. Malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na ci gaba da yajin aiki.
  7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata bakwai ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi har yau shiru.
  8. Jiya na yi korafin na sayi katin MTN ta bankina, an cire kudin ban ga katin ba. To daga baya na ga dari huduta ta koma asusuna. Ban daddara ba na kuma gwada saye, tun jiya da safe, kudin ya tafi amma har zuwa yanzun ba kati babu dalilinsa.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Da yake ana ta satar mun takalma a masallaci musamman a sallar asubah, sai na tsiri zuwa da takalmi hadin bauta. Ban tsira ba aka kwashe. Ina zuwa da tsofaffin takalma, su ma aka dinga sacewa. Ni tsiri sa silifas, su ma aka dinga sacewa. To a yanzun sai idan na je masallaci sai in bar kafa daya a waje, in shiga da kafa daya cikin masallaci, ko in ajiye a taga ko in dora a wani katako da ake dora takalma a cikin masallacin. To jiya da asubah an idar da sallah, na fito da kafa dayan, na tarar ba wacce na bari a waje. Da yake jama’a sun san an saba satar mun takalma da asubah, sai aka taya ni nema. To akwai wani gini a kusa da kofar masallacin sai wani ya daga idonsa sama, sai ya hango an dora shi a sama. Da yake wanda ya ga takalmin ya fi ni tsawo ya ciro mun. Nan kowa ke ta kawo nasa THEORY / RA’I a kan takalmin. Wani ya kawo Theory cewa ko ni na manta na dora. Matsalar wannan Theory ginin ya fi tsawon hannuna. Wani ya kawo Theory cewa yanzun haka barawon ne ya dora a sama tunda bai ga dayan ba da nufin idan an watse ya dawo neman dayan. Wani ya kawo Theory cewa watakila wani ne ya fito ya ga kafa daya tunaninsa tun sallar jiya mai shi ya bar shi a wajen saboda bai ga daya kafar ba, shi ne ya taimaka ya sa a sama.
Mai bibiyata kai wanne Theory ne ya zo maka a rai a kan wannan takalmi nawa? Ga ladan can ya soma kiran sallah domin kuwa yanzun karfe hudu da minti hudu na asubah.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply