Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, goma sha shida ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da hudu ga watan Oktoba, shekarar 2020.

 1. Akwai sabbin harbuwa da kwarona 160 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Ribas 42
Legas 32
Filato 21
Abuja 18
Kaduna 14
Ogun 11
Katsina 10
Kwara 3
Ondo 3
Imo 3
Anambara 1
Abiya 1
Oyo 1

Jimillar da suka harbu 59,287
Jimillar da suka warke 50,718
Jimillar da ke jinya 7,456
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,113

2.. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba wuta. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

 1. Yawancin ma’aikatan gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin an ci yaki an barsu da kuturun bawa. An yi bikin samun ‘yancin kan Nijeriya an bar su har zuwa yau ba albashi babu dalilinsa.
 2. Sojojin sama sun ce sun kai farmaki wurare guda biyu Maima da Tusaye da ke kusa da Dikwa da ke jihar Barno suka kashe ‘yan kungiyar Boko Haram da dama da lalata musu muhalli da kayan yaki.
 3. Sojojin Nijeriya da na kasar Kamaru na kokarin hada karfi don yakar ta’adanci.
 4. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya tura wani ayari na jami’an tsaro don kula da zaben gwamna na jihar Ondo da ke karatowa. Da bayanin babu wani dan sanda da zai yi wa wani babban mutum rakiya zuwa rumfar kada kuri’a ko wajen zabe.
 5. Hukunar shirya jarabawa ta JAMB ta ce ta bullo da wani sabon tsari na magance satar bayanan wani a mayar da su na wani.
 6. A jihar Filato an kama wadanda suka kashe basaraken Gundumar Foro.
 7. Al’umomin jihar Kogi na ci gaba da fama da ambaliya.
 8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata bakwai ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
 9. Wasu malaman jami’o’i watansu uku zuwa hudu ke nan ba albashi, sannan sauran ma’aikatan na shirin soma yajin aiki na gargadi.
 10. Ana ci gaba da bayanin shakiyancin da Donald Trump ya yi wa Joe Biden a ranar farko da suka fito suna muhawara. Inda Trump ke yi wa Biden tsiyar yana yawo da katon takunkumi kamar kura wai yana tsoron kwaronabairos. Sai ga shi Donald Trump da matarsa sun harbu da cutar shi Biden kalau.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ina da wata naira dari hudu a bankina, sai na sayi katin MTN na dari hudun. Tabbas an zare naira dari hudun daga ajiyata ta banki amma har zuwa yanzun da nake wannan rubutu karfe biyar saura minti ashirin na asuba ba katin babu dalilinsa.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply