Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, goma sha biyar ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da uku ga watan Oktoba, shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba wuta. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  2. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi addu’ar Allah Ya ba Shugaban Amurka Donald Trump da matarsa Melane lafiya sakamakon harbuwa da suka yi da kwaronabairos.
  3. Gwamnatin Tarayya ta umarci makarantu manya da kanana nata su koma makaranta ranar goma sha biyu ga watan nan. Su kuma makarantu na jihohi da masu zaman kansu gwamnati ta ce za su iya komawa a lokacin da suka ga sun shirya. Sai dai wasu na cewa an fahimci umarnin na Adamu Adamu ta baibai. Shi cewa ya yi an umarci UNITY SCHOOLS su koma.
  4. Shugaban Malaman Jami’o’i Farfesa Biodun ya ce gwamnatin tarayya na da ikon ce wa jami’o’i su koma, sai dai ba ta da ikon tilasta wa malaman komawa tunda ba ta ce musu komai ba, a kan yajin aikin da suke kai.
  5. Kungiyoyin manyan ma’aikata da kanana da ke aiki a jami’o’i, za su soma yajin aiki na gargadi na mako biyu daga biyar ga watan nan na Oktoba, wato daga jibi litinin ke nan.
  6. Gwamnatin Tarayya ta ce alfanu na tattalin arziki, da dinbin dama ta aikin yi da saukin kai komo na kayayyaki tsakanin Nijeriya da sauran kasashe, ya sa za a yi titin dogo daga Kano zuwa Maradi ta kasar Nijar.
  7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata bakwai suna dakon ariyas na sabon albashi.
  8. Wasu ma’aikatan kwalejojin foliteknik sun ce Nijeriya ta yi bikin cika shekara sittin da samun ‘yancin kanta, sai dai biki ya kare ba albashi wato dilin-dilin babu dalilinsa har zuwa yau.
  9. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 126 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 62
Ribas 22
Ogun 9
Filato 7
Abuja 7
Oshun 5
Kwara 5
Taraba 3
Bayelsa 2
Abiya 2
Zamfara 1
Imo

Jimillar da suka harbu 59,127
Jimillar da suka warke 50,593
Jimillar da ke jinya 7,422
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ga rubutun da na yi rana mai kamar ta yau, 3/10/2018 wato shekara biyu ke nan kamar haka:

‘Jama’a barkanmu da asubahin laraba, ashirin da uku ga watan Muharram, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da uku ga watan Oktoba, shekarar 2018.

Labarin farko Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ba za su taron Majalisar Zartaswa na wannan larabar kamar yadda suka saba ba, don bai wa ‘yan majalisar damar ci gaba da halartar zabukan fid-da-gwani da ake kan yi a halin yanzun.

Labari na biyu, kotu ta yi watsi da korafin da Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya ya kai cewa Majalisar Dattawa ba ta da ikon tilasta masa gurfana a gabanta.

Labari na uku wata tankar mai ce ta yi bindiga a babban hanyar da ke tsakanin Legas da Badagiri har motoci da dama aka ce sun kama da wuta.

Labari na hudu tun shekaranjiya har zuwa yanzun ake ta habaici da zambo a soshiyal midiya a farfajiyar siyasar jihar Kaduna. Habaicin, da zambo, da karin magana sun fi yin kamari ne jiya. Shekaranjiya dai na tare da Gwamna ne ke ta yi wa Sanata Hunkuyi iya shege cewa yana bugun kirjin shi ne jigon siyasa a jihar Kaduna, amma dubi yawan kuri’ar da ya samu da ba ta taka kara ta karya ba. Har ila yau, na tare da Ramalan Yero na cewa Isah Ashiru ai kifa daya kwal ne wato ba zai iya kayar da El-Rufai ba. To jiya tsakanin masu goyon bayan Shehu Sani ne, da masu goyon bayan El-Rufai da wanda ya so ya tsayar sanata wato Uba Sani ake ta habaici bayan nasarar Shehu Sani. Da mutum zai leka fesbuk sai ya samu sabbin habaici da zambo da karin magana da shagube da na tare da Shehu Sani ke ta jifar daya bangaren na El-Rufai da Uba Sani da su. Ni dai ba a ji mutuwar sarki a bakina ba.

Na yi nan kuma mu yini lafiya’

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply