Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, goma sha hudu ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da biyu ga watan Oktoba, na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Ana ci gaba da sharhi a kan cikar Nijeriya shekara sittin da samun ‘yancin kanta. Haka nan ana ci gaba da sharhi a kan jawabin da shugaban kasa Muhamadu Buhari ya yi wa ‘yan Nijeriya jiya da safe. Inda a jawabin, daidai inda yake bayanin a duniya dan Nijeriya ne ya fi sayen mai da arha, ya fi daukar hankalin jama’a har da PDP. PDP ta ce Buhari ya raina hankalin ‘yan Nijeriya ne da ya tsaya yana fadin a Saudiya ana sayar da kowacce litar mai kwatankwacin naira dari da sittin da takwas, a Nijeriya kuwa naira dari da sittin da daya ne. Suka ce a Saudiya mafi kankantar albashi naira dubu dari uku da ‘yan kai ne, kwatankwacin Riyad dubu uku. Suka ce a Nijeriya mafi kankantar albashi nawa ne? An ma kasa biya har yau.
  2. Kidinafas na ci gaba da bi unguwa-unguwa da gida-gida da ke ciki da wajen garin Kaduna suna dibar jama’a son ransu. A shekaranjiya kawai sun bi gida-gida sun kwashi jama’a a yankin Mando da ke cikin garin Kaduna da wuraren karfe biyu na dare, sai kuma wuraren Zangon Shanu da ke Zariya inda suka je wuraren karfe goma sha daya na dare suna yi wa jama’a a tara a tara suka kwashi jama’a suka yi gaba da su.
  3. Akwai sabbin harbuwa da kwarona su 153 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 81
Ribas 21
Abuja 11
Ogun 8
Kaduna 7
Oyo 6
Akwa Ibom 5
Oshun 3
Katsina 3
Edo 2
Ebonyi 2
Nasarawa 2
Filato 1
Kano 1

Jimillar da suka harbu 59,001
Jimillar da suka warke 50,452
Jimillar da ke jinya 7,437
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,112

  1. Yawancin ma’aikata na gwamnatin tarayya na korafin an yi bikin cikar Nijeriya shekara sittin da samun ‘yancin kai ba albashi babu bayaninsa.
  2. A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito an jima da safe don karanta shafukana na labarun da na kawo muku daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ga korafin da wasu likitoci suka turo mun kamar haka:

‘Assalamu Alaikum
Muna da korafi guda biyu

  1. Ana wasa da albashin manyan likitoci dake Asibitin koyarwa na Barau Dikko. Ana yawan zare musu specialist allowance. Ana yawan alakantashi DA laifin computer
  2. Sannan Akwai wani department a KASU college of medicine dasuka ki daukan kwararrun likitoci sai mutum daya dukda akwai wasu a kasa’

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2718373231768404&id=2356865571252507
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta