Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, gona sha uku ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da daya ga watan Oktoba na shekarar dubu biyu da ashirin.

Yau Nijeriya ke cika shekara sittin da samun ‘yancin kanta. Kuma an jima da karfe bakwaj na safe shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi wa al’umar kasar nan jawabi kai tsaye ta kafofin watsa labaru.
Sai dai da farko dai ‘yan Nijeriya da dama sun wayi garin yau ranar samun ‘yancin kan cikin jimami wasu kuma cikin jin dadi. Misali rabonmu da wutar lantarki tun jiya da safe, haka muka yini jiya, muka kwana har zuwa asubahin nan da nake wannan rubutu karfe hudu na asubah da wasu mintoci babu wutar. Ka ga Nijeriya ta cika shekara sittin talakanta na biyan kudin zama a duhu. Kodayake na ga sanarwa daga kamfanin lantarkin cewa ya rage kudin zama a duhu daga jiya da rana kamar yadda gwamnati ta ba da umarni

Na biyu yawanci sun wayi gari a hannun kidinafas. Misali a Kasuwar Magani da ke jihar Kaduna wata mata da goyonta na can hannun kidinafas ana cikinta har ciniki ya kai miliyan bakwai kidinafas sun ce ba su sallama ba. Ko shekaranjiya da daddare sun tsare tsakanin Kujama da Kasuwar Magani da ke jihar Kaduna sun kwashi mutane masu yawan gaske.

Na uku Najeriya ta wayi gari ‘yan boko haram na yi wa gwamna kwanton bauna suna neman sa’arsa. Su kashe sojoji su kashe ‘yan sanda ba ma ta talaka suke yi ba.

Na hudu yawancin ma’aikata sun wayi garin yau ba albashi babu dalilinsa. To jiya ina ABU Zariya, malaman ke sheda mun wasunsu wata hudu ke nan ba albashi. Haka jiya wasu likitoci daga asibitin Barau Dikko da ke nan Kaduna suka turo mun sakon duk wata sai an musu keange a albashi. Ga masu bin ariyas kusan shekara biyum misali ma’aikatan foliteknik.

Na biyar talakan Nijeriya zai wayi garin yau cikin tsadar abinci. Kodayake gaskiya abinci ya soma sauki. Misali masarar nan da na sayo kwatan buhu naira dubu shida mako biyi, a yanzun naira dubu biyar ce. Jiya muna idar da Sallar asubah wata mata ta matsa kofar masallaci tana kuka mijinta ya tsere bayan kullen kwarona ya barta da yara, ba abinci a taimaka mata. To da za ka yi wanka ka taka zuwa kasuwar bacci sai mutum a kalla biyar ya tare ka cewa ya baro gida bai ba iyali komai ba ka agaza masa.

Na shida yau asibitocin gwamnati sun gagari talaka. Idan mutum yana da ja ya leka asibitin Shika ko na Yusuf Dantsoho sai ya zubar da hawaye. Jiya ina ABU na ji wani malami na korafin za a yi wa iyalinsa aiki ana bukatar naira dubu dari a asibitin Shika kuma cikin gaugawa ake bukatar aikin. Mutumin yana cikin ‘yan wata hudu ba albashi.

Na bakwai, talakan Nijeriya zai wayi gari ba shi da hanya mai kyau. In mota gareka misali mu a nan Kinkinau da ke hawa mota Honda, duk inda ka fita ka dawo har sau biyar to kafafuwan motarka sun shiga uku tare da aljihunka. Yawancin masu keke nafef ba sa son zuwa Kinkinau. An kuma ji yadda nake ta godo da shugaban karamar hukumar Kudan a kan gadar Guibi da batun hanya da na wuta.

Na takwas talaka zai wayi gari ‘ya’yansa na gida ba boko ba Islamiyya. Sallar ma da kyar da jibin goshi mahukunta suka ga dama suka bari ana yi. An fake da kwarona.

Na tara yawancin ‘yan kasuwa za su wayi garin yau a talauce. Misali ina ‘yan kasuwar bacci? Ina na kasuwar Ceceniya ko Shek Gumi duk da ke cikin garin Kaduna? Je ka sami na kasuwar Shek Gumi ka ji korafin da yake yi. Haka nan kasuwannin kauye ba da ciwuwa saboda kidinafas sun kasa sun tsare.

Na goma talakan Nijeriya zai wayi gari da ci gaba da fama da ambaliya.

Na goma sha daya dan talaka da ya yi karatu, zai wayi gari yana ci gaba da neman aiki. Misali sa sanarwa za a dauki mutum goma aiki, sai ka ga mutum dubu goma a wajen. Kuma dan talaka ne ba dan sanata ba.

Na goma sha biyu talaka zai wayi gari ya saci kaza a tsare shi shekara biyar ba beli. Manyan na satar biliyoyi suna nan suna walarwarsu.

Yanzun karfe biyar na asubah ga ladan can da zakara suna rige-rigen samun lada.

Mu wayi gari lafiya.

Af! A rana mai kamar ta yau a shekarar 2016 na yi wannan rubutu da ke biye:

‘Jama’a barkanmu da asubah da fatan mun wayi gari lafiya? Yau Nijeriya ke cika shekara 56 da samun ‘yancin kanta daga turawan mulkin mallaka na Ingilishi. Wasu sun ce har yanzun ba a samu ‘yancin kan ba ana nan a kangin turawa shi ya sa aka kasa gane kan ci gaban kasar. Daga samun ‘yancin kan na Nijeriya zuwa yau Nijeriya ta yi mazaje daban-daban. Wasu aka kashe su, wasu suka mutu a kan mulkin wasu suka kwace mulkin, wasu suka gaji mulkin, wasu suka murde mulkin, wasu aka zabe su. Haka dai ake ta mazayawa da dadi ba dadi. To Allah Ya mana da kyau Amin. Hausawa sukan ce kar fa Kiru ta ja Bau.l(Kilu ta ja Bau. Na sa Kiru ne don labarin ya tafi daidai wa daida don na ga har an fara ci na gyara)To da alamu a yanzun Bau ce ta ja Kiru. Abdulmuminu Jibrin ke wakiltar mazabar tarayya ta Kiru da ke Kano a Majalisar Wakilai da a yanzun wasu ke ce mata Majalisar Yakubu Dogara. Sun dakatar da shi, shi kuma ya ci gaba da fasa kwai. Allura na tono garma. Fallasar sirrin Majalisar ta kankama. Yana ta tona musu asiri. Mutuncin da ake cewa madara idan ya zube shi ke nan. To tabbas mutuncinsu na ci gaba da zubewa. Ina mafita? Kuma matsala ce ta APC. Shin ita APC ba ta iya warware matsala cikin ruwan sanyi ba ne? To a yanzun wane ne mai gaskiya Jibrin ko Majalisar Yakubu Dogara? Ko a yi wa tufkar hanci tun yanzun ko ko ko ko ko hmmm. Na yi shiru. Mu yini lafiya’

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta