Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, goma sha biyu ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da talatin ga watan Satumba, shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Gobe take daya ga watan Oktoba, wato Nijeriya ta cika shekara sittin daidai da samun ‘yancin kanta. Gwamnatin tarayya ta ba da goben a matsayin ranar hutu. Sai dai kamar yadda gwamnati ta ce bikin ba zai yi armashi ba, haka ma’aikata da dama za su waiwayi ranar cikin babu saboda ba dilin-dilin.
  2. Kamfanonin raba wutar lantarki af! Kamfanonin karbar kudin zama a duhu sun ce ba su da masaniyar gwamnati ta janye karin kudin zama a duhu. Shi ya sa suke ta sayar da katin kudin zama a duhu har zuwa yau da dan karen tsada, da ci gaba da shiga unguwanni suna yankar wayoyin wadanda ba su je sun biya kudin zama a duhu ba.
  3. A makon gobe idan Allah Ya kai mu shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da daftarin kudirin kasafin kudi na shekarar dubu biyu da ashirin da daya, don dorewa da tsarin tabbatar da kasafin shekara na fara aiki daga watan Janairu ya kare Disamba. Da ma jiya ‘yan majalisar dattawa da ta wakilai suka koma majalisa bayan hutu na kusan wata biyu. Har a majalisar wakilai aka tayar da jijiyoyin wuya a kan sabuwar dokar ruwa ta kasa da wani dan majalisar ya ce ba a bi ka’dar majalisa ba wajen yin dokar.
  4. Sanata Elisha Abbo da kotu ta yanke masa hukuncin sai ya biya matar da ya ci zarafinta naira miliyan hamsin, ya ce zai daukaka kara don bai yarda da hukuncin ba.
  5. Shugaban Kasa ya mika wa majalisar dattawa sunayen wasu masu shari’a da yake son su amince masa ya nada su alkalan kotun koli, da kuma sunayen wasu jakadu.
  6. Gwamna Zulum na jihar Barno ya zanta da iyalan jami’an tsaron da aka kashe cikin ayarinsa a lokacin da aka kai musu hari.
  7. Jihohin Bayelsa, da Edo, da Kabbi, da Neja, su ma za su koma makaranta a mako mai zuwa. Daga firamare har manyan makarantu na jihohin.
  8. Wata kotun Ingila ta ba da umarnin a mayarwa da Nijeriya wata dala miliyan dari biyunta da aka tilasta mata biya a kan shari’arta da kamfanin nan na P&ID da aka gano damfarar Nijeriya aka yi da hadin bakin wasu ‘yan Nijeriya.
  9. Kotu ta yi watsi da bukatar Mai Lafiya ta a hana ‘yan sanda ci gaba da damunsa da tambayoyi.
  10. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafi a kan gadarsu da ta karye, da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  11. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida suna dakon ariyas na sabon albashi.
  12. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 187 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 74
Filato 25
Ribas 25
Gwambe 19
Abuja 19
Oshun 10
Kaduna 5
Barno 3
Ogun 2
Katsina 2
Nasarawa 1
Bayelsa 1
Edo 1

Jimillar da suka harbu 58,647
Jimillar da suka warke 49,937
Jimillar da ke jinya 7,599
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,111

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ranar 30 ga watan Satumba, na shekarar 2017 , yau shekara uku daidai na wayi gari a cikin garin Keffi na jihar Nasarawa. Ga rubutun da na yi da karfe hudu da wasu mintoci na asubah kamar haka:

‘Jama’a barkanmu da asubahin asabar, tara ga watan muharram, shekarar 1439 bayan hijirar cikamakin annabawa, kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da talatin ga watan satumba na shekarar 2017.
Tafiya mabudin ilimi. Yanzun haka ina wannan rubutu ne daga Keffi ta jihar Nasarawa. Na baro Kaduna jiya da yamma na bi hanyar nan ta Abuja, don ganin yadda tsaro ke tafiya, na shiga Abuja, na yi wasu sabgogi, na zarto Keffi.
Ina ta kokarin kwatanta Kaduna da Keffi.
Da farko dai tunda na shigo Keffi har zuwa yanzun da nake wannan rubutu ban ga kyallarowar wutar lantarki ba. A duhu muke. Na biyu, da ake ruwan sama da daddare, matan gidan da na sauka na ta tara bokitai da robobi. Na tambaye su, a Keffi ma ba ruwan famfo ne? Suka ce tsohon labari. Tun zamanin tsohon gwamna rabon da su ga ruwan famfo. Na lura ba hanyoyi ma su kyau a garin. Suka ce kwarai ba su da hanyoyi masu kyau. Yadda na ji dadin garin ban ji sauro ko daya ba.
Sannan da hudu ta asubar nan ta yi na kasa kunne in ji ladan na kiran assalatu. Ban ji ko daya ba, sai wasu zakaru biyu na ji suna cara. Ko ladanan sun makara ne, ko kuma lokacin ne ya sha bamban da Kaduna? Yanzun karfe hudu da minti ashirin na ji wasu kide-kide na tashi shigen na wuraren ibada na abokan zama.
Jama’a mu yini lafiya’

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2716403081965419&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply