Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Asaalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, ashirin da uku ga watan Zulkida, shekara ta 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S A.W. Daidai da goma sha biyar ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci karamin ministan kwadago Keyamo da suka yi sa-in-sa da ‘yan majalisar dokoki ta tarayya, da ya share ‘yan majalisar ya yi aikin da ya sa shi na daukar mutum dubu dari bakwai da saba’in da hudu, wato mutum dubu daya a kowacce karamar hukuma ta kasar nan aiki a wani tsari na musamman na tallafawa.
 2. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike da wani ayarinsa na musamman zuwa Amurka a kan batun sake zabar Adesina.
 3. Nijeriya ta samu dala biliyan dari biyu da shida daga danyen man fetur a shekaru biyar da suka gabata.
 4. Majalisar Datrawa ta kama hanyar gyaran dokar duk wanda aka kama da laifin kidinafin a masa daurin-rai-da-rai, a batun masu fyade kuma dokar hukunta su ta shafi maza da mata ba maza kadai ba, da rashin iyakance shekaru.
 5. Majalisar Wakilai ta ce za ta binciki batun ajiye aiki na wasu sojoji dari uku da sittin da biyar da ke zargin rashawa da wasa da kula da jin dadinsu.
 6. Majalisar Wakilai ta ce sam ba ta yarda a ce wasu dalibai ba za su rubuta jarabawar WAEC ba a kasar nan , tare da bukatar gwamnati ta saura shawara a bar kowa ya rubuta.
 7. An kwaso rukuni na uku na ‘yan Nijeriya da ke Ingila.
 8. Kungiyar kasashen da ke da arzikin manfetur OPEC ta ce Nijeriya ce ta biyu bayan Saudiya a cikin kungiyar, da arzikinsu na samu GDP ya fi karuwa a shekarar 2019.
 9. Hafsan hafsoshin mayakan kasa na kasar nan Tukur Buratai ya sake yin wasu manyan sauye-sauye na janar-janar guda talatin da bakwai, da kanal-kanal biyar.

9, Tsohon shugaban kasa Jonathan ya jagoranci wasu mukarrabai na musamman na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS zuwa Mali.

 1. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’ duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata uku ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
 2. Gwamnan jihar Delta Ifeanyi, da matarsa da duk sauran iyalansa da suka harbu da kwaronabairos sun warke.
 3. A duniya bakidaya mutum miliyan goma sha uku ya harbu da kwaronabairos.
 4. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci, akwai mutum dari hudu da sittin da uku da ya harbu da kwaronabairos a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 128
Kwara 92
Inugu 39
Delta 33
Edo 29
Filato 28
Kaduna 23
Oyo 15
Ogun 14
Oshun 14
Abuja 12
Ondo 9
Ribas 9
Abiya 8
Bayelsa 6
Ekiti 3
Barno 2

 • Kaduna 23 Kano ?

Jimilar wadanda suka harbu a Kaduna zuwa jiya da daddare 1039.

Jimilar wadanda suka harbu 33,616
Jimilar wadanda suka warke 13,792
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 754
Wadanda ke jinya 19,070

Mu wayi gari lafiya.

Af! Allah Ka raba mu da sharrin mutum Amin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply