Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, tara ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da bakwai ga watan Satumba shekarar 2020.
- Gobe litinin idan Allah Ya kai mu za a wayi gari da yajin aiki na kugiyoyin kwadago da ke fadin Nijeriya, a kan karin kudin zama a duhu da karin kudin mai. Wasu bayanan da ke umarnin dakatar da yajin aikin da gwamnati ta nema wajen kotu, ta kuma ba ta, takardar umarnin ba ta isa hannun kungiyoyin kwadagon ba. Ma’aikatan sufurin jiragen sama, da na shari’a, da na bankuna da sauransu duk sun ce za su amsa kiran kungiyoyin kwadago. Can kuma wani bayani ke umartar manyan ma’aikatan gwamnati daga mataki na goma sha biyu zuwa sama, su je aiki.
- Jiya ma mun wayi gari ba wuta, mun yini ba wuta, mun kwana har zuwa asubahin nan ba wuta. Kuma dole in wata ya kare talaka ya je ya biya kudin zama a duhu. Zama kuma mai tsada a yanzun.
- An sako tsohon jakadan Nijeriya a Venezuela/Benezuwela Felix bayan ya kwashe mako uku a hannun kidinafas.
- A jihar Nasarawa jami’an tsaro sun kashe kidinafas uku suka ceto mutum biyun da suka yi kidinafin.
- An soma gina wuraren soja da na ‘yan sanda a kan iyakar Taraba da Binuwai ko a samu sa’idar fada tsakanin Munci da Jukunawa.
- Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba wuta. Ga tsadar taki ga ambaliya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida suna dakon ariyas na sabon albashi.
- Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 136 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 41
Ogun 27
Ribas 19
Abiya 10
Oyo 6
Filato 6
Bauci 5
Ondo 5
Ekiti 4
Kaduna 4
Edo 3
Ebonyi 2
Bayelsa 1
Delta 1
Oshun 1
Yobe 1
Jimillar da suka harbu 58,193
Jimillar da suka warke 49,722
Jimillar da ke jinya 7,365
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,106
Mu wayi gari lafiya.
Af! Na samu labarin mutane na ta zuwa nemana gidan rediyon sifaida ‘yaf’yam, rediyon da na shugabanta na dan wani lokaci, na kuma yi masa manaja na shirye-shirye. To aikin da aka tura ni na dora rediyon a turba ta ci gaba ya kare, har wadanda suka tura ni suka yaba da dinbin nasarorin da na samu, suka dauke ni. Wato a yanzun ba na tare da gidan rediyon ina ma hutun karatu. Sai dai wannan dama ce ga wadanda ke shirin kafa sabon gidan rediyo ko talabijin ko ma suke da shi suke bukata a saisaita musu shirye-shirye na rediyon ko talabjin, su tintibe ni. Kada a manta na horas da ma’aikatan:
Rediyon Nijeriya na Kaduna FRCN
Gidan Talabijin na NTA
Gidan Rediyon KSMC
Gidan Rediyon Nagarta
Gidan Rediyon Freedom
Gidan Rediyon Liberty
Gidan Rediyon Jami’ar jihar Kaduna
Gidan Rediyo Da Talabijin na Alheri da DITV
Kafar Labaru ta NewAge Network
Kafar horas da ma’aikatan rediyo da talabajin ta Kaduna Media Academy
Kungiyar NUJ
Da sauransu. Ina ba da takardar shaidar samun horo daga gare ni da ke da daraja.
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.