Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikun barkanmu da asubahin laraba, biyar ga watan Safar, bayan hijirar cikamakin Annabwa kum fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. daidai da ashirin da uku ga watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 176 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 73
Filato 50
Abuja 17
Ribas 8
Ondo 6
Neja 5
Ogun 5
Edo 3
Kaduna 3
Oyo 2
Bauci 1
Bayelsa 1
Delta 1
Nasarawa 1

Jimillar da suka harbu 56,613
Jimillar da suka warke 48,836
Jimillr da ke jinya 7,677
Jimillar da ke jinya 7,677
Jimillar wadanda suka riga mu gidan gaskiya 1,100.

  1. Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta mika wa gwamna Obaseki takardar shaidar sake lashe zabensa.
  2. Tsohuwar Shugabar Kasar Laberiya Ellen Johnson ta jinjina wa Rochas Okorocha da ke bikin cika shekara hamsin da takwas da ya yi a duniya.
  3. Gwamnan jihar Barno Zulum ya sanar da gudunmawar naira miliyan ashirin da gida ga iyalan wani Birgediya Dahiru Bako, kwamandan wata runduna ta musamman ta ashirin da biyar da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kashe wani kwanton-bauna da suka yi wa sojoji a hanyar Demboa.
  4. Wasu kidinafas sun kai hari a jihar Nasarawa suka kashe mutum guda, suka yi kidinafin mutum goma da ji wa wasu da dama rauni.

.6. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna na can suna ci gaba da kasancew a killace shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba wuta. Ga tsadar taki ga ambaliya. Ga gadar da sukan samu su hara ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan, Jaja, ya musu alkawari ifan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

  1. Yau ranar hutu ce ga ma’aikatan jihar Kaduna, da Gwamna ya ba da hutun don yau uku da rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dafta Shehu Idris. An ba da hutun don zaman makoki.
  2. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i sun ce shekara daya da wata shida suna jiran ariyas.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ga wadanda ke iya gani hoto idan na sa, hoton da ke biye da rubutuna na yau, aikin shinkafa mutanen Guibi ke yi.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya

Labarai Makamanta

Leave a Reply