Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, hudu ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyu ga watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Jam’iyyar APC ta taya Gwamna Obaseki murnar sake lashe zaben gwamnan jihar Edo karkashin jam’iyyar PDP.
  2. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 195 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Inugu 51
Gwambe 40
Legas 39
Filato 23
Abuja 15
Ribas 12
Kaduna 8
Ondo 3
Bauci 2
Edo 1
Ogun 1

Jimillar da suka harbu 57,487
Jimillar da suka warke 48,674
Jimillar da ke jinya 7,713
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,100

  1. Majalisar Dinkin Duniya na bikin cika shekara saba’in da biyar da kafuwa, inda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya lasafto dinbin gudunmawar da Nijeriya ta bayar ga ayyukan majalisar, har da ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasashen duniya da Nijeriya ta taka rawar gani.
  2. Saboda matsin lambar ECOWAS sojojin Mali da suka yi juyin mulki sun nada tsohon ministan tsaron kasa wani BaNdado, Kanal mai ritaya a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya, shi kuma jagoran sojojin da suka yi juyin mulkin a matsayin mataimaki.
  3. ‘Yan sanda sun ceto sauran jami’an hukumar kiyaye hadurra su shida da suka yi saura a hannun kidinafas, da kidinafas din suka yi kidinafin su wajen ashirin da bakwai a jihar Nasarawa.
  4. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba wuta. Ga tsadar taki ga ambaliya. Ga gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  5. Hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano na shirin gabatar da wasu tuhume-tuhumen da take yi wa Sarkin Kano Sanusi na biyu.
  6. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida suna dakon ariyas na sabon albashi. Wasu malaman jami’a ma wata da watanni ba albashi.
  7. Malaman makaranta da iyayen yara sun yi zanga-zanga a jihar Kwara, ta nuna bacin ransu a kan ci gaba da rufe makarantu masu zaman kansu a jihar da sunan kwaronabairos.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Gabadaya yinin jiya, har zuwa karfe hudu na asubahin nan da nake wannan rubutu, ina ta jiran wutar lantarki ta yi karfi in yi wani aiki, aiki kuma muhimmi har yanzun kyandir ya fi ta kumari. Kuma ga kudin wutar an ninka ninkin ba ninki. Af! Ga wani can yana tuna mun cewa in ce an ninka kudin zama a duhu dai.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply