Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, daya ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha tara ga watan Satumba na shekarar 2020.
- Kwamitin da ya saba raba kudi tsakanin gwamnatin tarayya, da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi FAAC a duk wata, ya raba naira biliyan dari shida da tamanin da biyu da ‘yan kai na watan Agusta, da ke nuna idan an yi sa’a a soma jin dilin-dilin zuwa karshen mako mai zuwa.
- Yau za a gudanar da zaben gwamnan jihar Edo. Har na ga Secondus na PDP na cewa rayuwar wasu gwamnonin PDP da suka je shaida zaben kuma suka sauka a wasu otel-otel na cikin hadari domin kuwa ana ta musu barazana ga rayuwarsu.
- Hukumar kula da al’amuran ‘yan sanda PSC a takaice, ta ce za ta sanya ido don ganin wacce irin rawa ‘yan sanda za su taka a zaben na jihar Edo da za a yi yau. Da ma shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya ce ya tura ‘yan sanda su fiye da dubu talatin jihar Edo don tabbatar da tsaro a zaben na yau.
- Dan Majalisar da ya gabatar da kudurin dokar gyara ga aikin dan sanda, Yusuf, ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda sanya hannu da ya yi a kan dokar ta ‘yan sanda ta shekarar 2020.
- Kungiyar Tarayyar Turayya E.U. a takaice, ta bukaci gwamnatin tarayya ta dage takaita zirga-zirgar jiragen sama na Turai zuwa Nijeriya kai tsaye da ta yi, inda ministan lafiya da na sufuri na Nijeriya suka ce Nijeriya ta takaita zuwansu nan kasar ne saboda tsoron kada su dinga yo tsarabar kwaronabairos suna jibge mana a kasa. Suka ce amma za a duba rokon.
- Ngozi Okonjo Iweala ta samu tsallakawa mataki na gaba, na yi wu war lashe zaben shugabancin babbar kungiyar kasuwanci ta duniya WTO a takaice.
- Gwamnatin jihar Neja ta sake bude hanyar Minna zuwa Bidda da masu jido mai daga Kudu zuwa Arewa ta motoci tanka suka yi korafin gwamnatin ta rufe musu, har suka yi barazanar daina jido man.
- Sojojin sama masu lakabin Operation Thunder Strike, sun kai hare-hare ta sama, dazukan jihar Kaduna, suka kashe ‘yan bindiga masu tarin yawa, da lalata tungarsu da kayayyakinsu.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
- Gwamnatin Tarayya ta ce a yi hakuri akwai gyara a umarnin da aka bayar na duk wanda ke da asusu na banki, ya je ya sake yi wa asusun nasa rajista da wasu bayanai.
- Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba wuta. Ga tsadar taki ga ambaliya. Ga gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar na Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 221 a jihohi da alkaluna kamar haka:
Legas 59
Abiya 56
Abuja 22
Gwambe 20
Filato 17
Ribas 11
Bauci 7
Binuwai 6
Ekiti 6
Imo 6
Kaduna 4
Kwara 4
Ondo 4
Ogun 3
Oshun 3
Bayelsa 1
Edo 1
Kano 1
Jimillar da suka harbu 56,956
Jimillar da suka warke 48,305
Jimillar da ke jinya 7,557
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,094
Mu wayi gari lafiya.
Af! Allah Ka raba mu da sharrin mutum Amin.
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.