Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, ashirin da tara ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha takwas ga watan Satumba, na shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ce ta kammala kai muhimman kayayyakin zabe jihar Edo, don gudanar da zaben gwamna da za a yi na jihar.
 2. Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ECOWAS, ta ce ta amince farar hula ya jagoranci shirye-shiryen mika mulki ga farar hula na tsawon wata goma sha takwas wato shekara daya da rabi a kasar Mali.
 3. Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya sanya hannu a kan sabuwar dokar yi wa duk namijin da kotu ta kama da laifin yi wa yara kanana fyade dandaka, in kuma mace ce aka kama da laifin, ko a juyar da mahaifarta ko daurin – rai – da – rai.
 4. Wasu ‘Yan bindiga sun kai hari wani ofishin ‘yan sanda da ke Gidan Mudi a jihar Sakkwato, suka kashe difi’on ‘yan sanda tare da wani.
 5. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
 6. Bayanai na nuna farashin masara da na shinkafa suna kankankan a kasuwa. Domin garin masarar kwatan buhu a yanzun ya haura naira dubu shida. Buhu ya zama naira dubu ashirin da hudu ke nan.
 7. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shawarci ‘yan siyasa na jihar Edo, su kauce wa neman mulki ta hanyar ko a mutu ko a yi rai.
 8. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, ya ba da umarnin takaita zirga-zirgar ababen hawa daga yau juma’a da daddare har zuwa lahadi da sassafe a jihar Edo.
 9. Rahotanni na nuna kashi biyar cikin dari na ‘yan Nijeriya da aka kwaso daga kasashen waje sun harbu da kwaronabairos, duk da takardun da suka zo da su na bayanin ba su da cutar.
 10. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da kasancewa a killace, shekara da shakaru ba hanya. Wata da watanni ba wutar lantarki, ga tsadar taki ga ambaliya, ga gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
 11. Gwamnan jihar Barno Zulum, ya ziyarci ‘yan Nijeriya su dubu dari da ashirin da shida da ke gudun hijira a sansanoni da ke kasar Nijar, da ake shirin kwaso su zuwa gida Nijeriya.
 12. A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fita an jima da safe, don karanta shafukana da ke dauke da labarun da na kawo muku, daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis.

Mu wayi gari lafiya, mu kuma yi juma’a lafiya.

Af! Har zuwa karfe uku da rabi na dare da nake wannan rubutu ina ta lekawa dandalin hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC don samo sabbin alkaluman wadanda suka harbu da kwaronabairos, ban ga ta sa ba kamar yadda ta saba sawa cikin dare. Sai dai a wuraren karfe uku da rabin na dare na ga tashar CHANNELS TELEVISION ta nuna akwai sabbin harbuwa 131, sai jimillar da suka harbu 56,735, sai jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,093

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta