Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, ashirin da takwas ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha bakwai ga watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin.
- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana tambarin bikin Nijeriya ta cika shekara sittin da samun ‘yancin kai. Ya kaddamar da tambarin ne a lokacin taron Majalisar Zartaswa na jiya laraba.
- Gwamnatin Tarayya ta amince a samar da wata hukuma da za ta alkinta ribar da aka samu daga masu aikata laifuka.
- Gwamnatin Tarayya za ta gana da Amurka a kan hanin da ta yi wa wasu ‘yan siyasar kasar nan da ake rade-radin har da su Ganduje da Oshiomhole da sauransu shiga Amurka.
- Gwamnatin Tarayya na shirin kwaso wasu ‘yan Nijeriya da suka haura Nijar gudun hijira.
- Kungiyar Kwadago ta Kasa ta ba Gwamnatin Tarayya wa’adin mako biyu ta janye karin kudin mai da na wutar lantarki da ta yi in ba haka ba a mata bore.
- Bayanai na nuna za a fara wahalar mai a jihohin Arewa saboda direbobin tankokin da ke dauko man daga Legas zuwa Arewa, sun dakatar da jido man saboda jihar Neja da sukan biyo ta cikinta, gwamnatin jihar ta hana su bi ta jihar. Da ke nuna ba wata hanyar da ta musu saura da za su iya biyowa don kawo man Arewa.
- Shalkwatar Tsaro ta ce sojoji sun kai farmaki ta sama, wasu muhallan ‘yan bindiga da ke jihar Zamfara, inda suka kashe da dama da lalata musu muhalli da kayan ta’addanci.
- Za a bude manyan makarantu da ke jihar Binuwai don ci gaba da karatu.
- Babban Bankin Nijeriya zai raba wa ‘yan Nijeriya marasa karfi su dubu dari tara har da yara, wata naira biliyan dari biyu a matsayin bashi na mallakar gida.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida suna dakon ariyas na sabon albashi. Wasu malaman jami’a ma watansu uku ke nan ba albashi.
- Wata kotu ta umarci likitocin da ke yajin aiki, su janye yajin aikin.
- Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba wutar lantarki. Ga tsadar taki ga ambaliya. Ga gadar da sukan samu su haura ta balle. Gadar da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Tinubu na ta jawabi a talabijin kada a zabi Obaseki ya sake zama gwamnan jihar Edo, saboda bai san wahala da gwagwarmaya da ciwon mulkin jihar ba, a sama ya tsinta ya kuma butulce musu.
- Kasar Sin wato Caina ta ce zuwa watan jibi maganin da ta samar na kwaronabairos zai karade duniya.
- A kwai sabbin harbuwa da kwarona 126 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Abuja 37
Legas 27
Filato 16
Kaduna 9
Abuja 7
Gwambe 6
Ondo 6
Imo 5
Delta 2
Ekiti 2
Kwara 2
Oyo 2
Bauci 1
Kano 1
Katsina 1
Ogun 1
Yobe 1
Jimillar wadanda suka harbu 56 604
Jimillar wadanda suka warke, 47,872
Jimillar da ke jinya 7,641
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,091
Mu wayi gari lafiya.
Af! A rana mai kamar ta yau, wato 17/9/2016 yau shekara hudu daidai na yi wannan rubutu:
‘Jama’a barkanmu da shiga karshen mako, makon da muka yi shagulgulan Sallah, da kuma cacar baki tsakanin jam’iyyar PDP da ta APC a kan mulkin kasar nan. Cacar bakin wato ‘COLD WAR’ da zan tabo yau. Ke PDP ke kika fara tsokanar fada cewa tunda Baba Buhari ya gaza ba zai iya ba ya sauka ya ba PDP wuri ta taho da kwararrunta na tattalin arziki domin ceto kasar.APC ta mayar wa da PDP martanin cewa wa ya jefa kasar cikin halin da ake ciki in ba PDP ba?An samu kudi na fitar hankali maimakon a alkinta a yi wasu ayyuka sai gafiyoyin PDP suka yi ta wawure dukiyar kasar. Sai PDP ta ce idan an ce ba ta yi komai ba wa ya yi titin jirgin da APC ta kaddamar zuwa Rigasa? Wa ya tsara zaben gaskiya har da APC ta dare mulkin? Har PDP ke cewa a koma da kasar yadda take da farashin dala da na shinkafa da farashin mai kamar yadda APC ta karbi mulkin ita PDP za ta dora a ga ko tattalin arzikin zai sukurkuce haka. APC ta ce karyar banza wato a mayar wa da kungiyar boko haram garuruwan ma da ta kwace su ci gaba da kashe jama’a da tashin bom ke nan ko? APC ta ce da tashin bom gara tashin dala da tsadar shinkafa da Audu Ogbe ya ce nan da karshen shekarar nan san an sayi buhun shinkafa naira dubu arba’in. Sai dai abin da na lura da shi ne yawancin mukarraban Baba Buhari da ke dora wa PDP laifin halin da ake ciki ‘yan PDP ne suka rikide suka koma APC. Shin a lokacin da suke PDP suna nufin ba da su aka hadu aka wawure dukiyar kasar da a yanzun suke da bakin zargin PDP ba? Su wane ne jigon PDP in ba su ba? To a yanzun ma su suke bata wa Baba Buhari gwamnati da gurbatattun shawarwari shi ya sa nake ta ankarar da Baba Buhari cewa yana kitso da kwarkwata a ciki
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.