Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, ashirin da bakwai ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha shida ga watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin.
- Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 90 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 33
Filato 27
Kaduna 17
Ogun 6
Abuja 4
Anambara 1
Ekiti 1
Nasarawa 1
Jimillar da suka harbu 56,478
Jimillar da suka warke 44,430
Jimillar da ke jinya 10,960
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,088
- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ciyo bashi don gudanar da ayyukan kyautata jin dadin ‘yan Nijeriya ba laifi ba ne.
- Mataimakin Shugaban Kasa Osinbanjo ya je Accra Ghana wajen wani taron kungiyar raya tattalin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, inda taron ya cimma matsaya a kan dole farar hula ne ba soja ba, zai jagoranci turbar mayar da mulki hannun farar hula a kasar Mali.
- Gwamnatin Tarayya da shugabannin kungiyoyin kwadago sun yi taro jiya, inda kungiyoyin suka bukaci gwamnatin tarayya ta janye karin kudin mai da na lantarki da ta yi ba tare da bata wani lokaci ba. Kungiyar ta ce duk wani kwatance da ake yi da sauran kasashe musamman yammacin Afirka, ta ce a dubi sauran kasashen suna da albashi mafi karanci abin da babu a Nijeriya. Ta ce nan an karya darajar Naira ba kamar sauran kasashe ba.
- Ministar kudi Shamsuna, ta ce babu gaskiya a bayanin da ministan labaru Lai Mohammed ya yi cewa wai abinci na ci gaba da arha a kasuwa. Ta ce gaskiyar batu shi ne abinci na tsada. Lai Mohammed ya je kasuwa ya gani.
- Hukumar Reliwe ta ce babu gaskiya a labarin da ake ta yadawa cewa ‘yan bindiga sun harbi daya daga cikin jiragen da ke zirga-zirga daga Kaduna zuwa Abuja. Ta ce jifa ce ta dutse ba harsashi ba kuma tuni aka gyara gilashin da dutsen ya tarwatsa.
- Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta kashe naira biliyan hudu a kan tsaro cikin shekaru shida da suka gabata.
- Hukumomi sun yi korafin matafiya na kasashen duniya na zuwa Nijeriya da takardar bogi da ke nuna an musu gwajin kwaronabairos.
- A karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, kidinafas sun kashe mutum guda, suka yi kidinafin mata goma.
- A dai jihar ta Katsina kidinafas sun kashe wani jami’in hukumar DSS bayan sun karbi kudin fansarsa naira miliyan biyar.
- Kidinafas sun sako mutane shida da suka yi kidinafin a Tungar Maje da ke yankin Abuja bayan an biya kudin fansa.
- Jami’an tsaro sun yi nasarar ceto jami’an hukumar kiyaye hadurra da kidinafas suka yi kidinafin a jihar Nasarawa. Sun ceto uku yanzun saura bakwai a hannun kidinafas din.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi. Wasu malaman jami’a na korafin watan su uku ba albashi.
- Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba titi. Wata da watannu ba wuta. Ga tsadar taki ga ambaliya. Gadar da sukan samu su haura ta balle. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzu, Jaja, ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Allah Ya yi wa Sarkin Biu Umar Mustapha rasuwa.
Mu wayi gari lafiya.
Af! Gaskiya sabuwar wutar lantarki da aka kara wa kudi ta fi ta da gudun fanfalaki. Kamar yadda na yi bayani kwanakin baya, katin naira dubu daya, ya koma naira dubu biyu a yanzun. Sannan kana sa katin, sai katin ya falla a guje kafin ka ankara ya kare. Kamar man fetur da aka kara kudinsa. Shi ma kana sa wa, da ka tuka motar nan zuwa can, sai ka ga shi ma ya falla a guje ka nemi shi ka rasa ba ya cikin tanki.
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.