Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, ashirin da biyu ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha hudu ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Gwamnatin Tarayya ta fitar da sharudda da ka’idojin sake bude makarantu.
 2. Gwamnatin tarayya ta ce a yanzun wanda zai hau jirgin sama, na iya zuwa tashar jirgin sama sa’a daya da rabi kafin jirgin ya tashi da shi, maimakon da, da aka ce dole sai ya isa tashar sa’a uku kafin tashin jirgin.
 3. Gwamnatin Tarayya ta umarci ‘yan kwangila da ke aikin samar da lantarki, su hanzarta komawa wuraren aikin.
 4. Benen cibiyar kasuwanci ta duniya da ke Abuja ya yi gobara jiya.
 5. Jirgin kamfanin Air Peace ya samu wani babban jirgi kirar Boeing don kwaso ‘yan Nijeriya su dari uku da ke Asia/Eshiya.
 6. Ranar goma sha uku ga watan nan na Yuli aka cika shekara biyar cur da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauke su Alex Badeh, da Usman Jibril da Kenneth Mimimah.
 7. Gwamnatin Tarayya ta ce cikin kwana goma sha shida, masu neman aikin N-Power su miliyan hudu da kusan rabi suka ciccike abubuwan da ake cikewa don nema.
 8. Babban Akanta na Kasa na so ya ji ta yaya hukumomin sojan ruwan Nijeriya suka kashe wata naira miliyan goma sha daya da rabi wajen hayar wani gida mai daki hudu a Ikoyi Legas, don a rasidin babu bayanin kudin na shekara nawa ne, kuma ba inda aka nuna an cire harajin tamanin kaya wato VAT.
 9. Ministan Shari’a Malami ya maka jaridar Sahara Reporters a kotu, yana zargin ta bata masa suna da wani zargi mara tushe.
 10. Magu ya shiga mako na biyu a zargi daban-daban da ake masa da ya musanta.
 11. Wasu ‘yan bindiga sun tare manyan tituna da ke Wukari a jihar Taraba suka kashe na kashewa.
 12. Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wasu al’umomi uku da ke yankin karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna, suka kashe mutum a kalla ashirin da hudu da kona gidaje da awon gaba da shanu.
 13. Wasu ‘yan bindiga sanye da kayan sarki, sun kwashi jama’a, maza da mata, suka kashe na kashewa a inda ake kira unguwar KKA da ke cikin garin Kaduna.
 14. Likitoci talatin da biyar suka harbu da kwaronabairos a jihar Kwara.
 15. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos, su 595 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 156
Oyo 141
Abuja 99
Edo 47
Kaduna 27
Ondo 22
Ribas 20
Oshun 17
Imo 13
Filato 10
Nasarawa 8
Anambara 8
Kano 5
Binuwai 5
Barno 5
Ogun 4
Taraba 3
Gwambe 3
Kabbi 1
Kuros Ribas 1

 • Kaduna 27, Kano 5 !

Jimilar wadanda suka harbu 33,157
Jimilar wadanda suka warke 13,671
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 744
Wadanda suke jinya 18,738

Mu wayi gari lafiya

Af! Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata uku ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.

Af!! Alllah Ya raba mu da sharrin mutum Amin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply