Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, ashirin da biyar ga watan Muharram, shrkarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halita, Annabi Muhammad S.A.W. da ya zo daidai da goma sha hudu ga watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 78 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 30
Kaduna 17
Ogun 7
Anambara 5
Kano 4
Katsina 3
Abuja 3
Akwa Ibom 3
Oyo 2
Ribas 2
Delta 1
Filato 1
Ondo 1

Jimilar da suka harbu 56,256
Jimillar da suka warke 44,152
Jimillar da ke jinya 11,022
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,082

  1. Za a wayi gari da yajin aikin dukkan ma’aikatan lafiya JOHESU, sai dai gwamnatin tarayya ta ce za fa ta yi aiki da dokar nan ta wanda bai je aiki ba, to ba shi ba albashi.
  2. Mutum a kalla uku suka riga mu gidan gaskiya, sai muhalli da gonaki da dama da ambaliya ta yi sanadiyyar asararsu duk a yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna.
  3. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar ta Kudan da ke jihar Kaduna, na ci gaba da kasancewa a killace, shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wuta, ga tsadar taki, ga ambaliya, ga gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzu, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan suka zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  4. Fadar shugaban kasa ta mayar wa da Obasanjo martanin sunansa da ma DIVIDER – IN – CHIEF da ba abin da ya iya sai raba kan ‘yan Nijeriya
  5. Mukarraban Gwamnatin Tarayya sun je yi wa mutanen jihar Kabbi da ambaliya ta yi wa ta’adi jaje a madadin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
  6. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan, suna zaman dakon ariyas na sabon albashi.
  7. Wasu malaman jami’o’i na korafin watan su na uku ke nan ba albashi.
  8. Ta tabbata talaka ya fara biyan sabon kudin wuta, da sabon kudin fetur, da tsadar komai ma na rayuwa na yau da kullum.
  9. Ana can ana ci gaba da rusau wa shaguna da ke gefen titi daga Samaru zuwa Tudun Wada da Sabon Garin Zariya.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Na ji wasu na korafin sun dauka an ce an hana almajirai yawon bara a jihar Kaduna? To ai mu a Kinkinau kullum da almuru har zuwa cikin dare za ka ji almajirai na ta bi gida-gida suna barar abinci. Suna cewa Allaziwahidun. Iya ko dan kanzo ne. Iya ko dan dago-dago ne. Iya ko gaya ne ba miya. Iya wallahi ban samu abinci ba. Wadanda ni ma na gani jiya sun zo bara ana yayyafi da yake jiya mun hada sallar magrib da Isha’i, yara ne ‘yan kanana abin tausayi da kadan suka girmi kakana Khalid.

Za a iya leka rubutun yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply