Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, ashirin da hudu ga watan Muharram na shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha uku ga watan Satumba, na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 160 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Abuja 39
Legas 30
Kaduna 23
Katsina 7
Ribas 6
Oyo 6
Yobe 6
Binuwai 3
Bayelsa 1
Abiya 1
Edo 1
Ekiti 1

Jimillar da suka harbu 56,177
Jimillar da suka warke 44,088
Jimillar da ke jinya 11,011
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,078

  1. Sai ranar talata mai zuwa shugabannin kungiyoyin kwadago na kasar nan za su kuma yin taro da ministan kwadago a kan karin kudin mai da na lantarki. Bayanai na nuna shugaban kasa ne da kansa ya nemi a yi wannan ganawa don sanar da kungiyoyin gaskiyar halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki na rashin kudi.
  2. Kungiyar Malaman Jami’o’i da ke yajin aiki, ta ce ta dai gano cewa burin gwamnatin tarayya shi ne durkusar da jami’o’i na gwamnati.
  3. Janar Tukur Buratai ya sanar da karin tsawon rawar da soja ke yi ta OPERATION SAHEL SANITY da aka kaddamar a nan Arewa a watan Yuni, don gamawa da kidinafas, da ‘yan bindiga, da sauran miyagun mutane da ke addabar Arewa, da aka tsara kammala rawar a watan nan na Satumba da muke ciki, a yanzun sai watan Disamba rawar za ta kare.
  4. Cif Olusegun Obasanjo ya ce kasar nan ta kama hanyar balbalcewa. Sai fa an yunkura don ceto ta.
  5. Ana ta zuwa Sakkwato don yi wa Wamakko gaisuwar ta’aziyyar rasuwar diyarsa da ta rasu a lokacin haihuwa.
  6. Su Ganduje, da Kwankwaso da Shekarau da Secondus da sauransu, na ta safa-da-marwa garin Bini don ganin yadda za su bullo wa zaben gwamna na jihar Edo da ake shirin yi.
  7. Ayuba Wabba ya ce a jira za a ji daga gare su a kan ko za a yi yajin aiki da bore ko ba za a yi ba, a kan karin kudin mai da na wutar lantarki da gwamnatin tarayya ta yi.
  8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi. Sai wasu malaman jami’o’i da ke korafin rabon su da albashi wajen wata uku ke nan.
  9. A jihar Bauci ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutum a kalla goma sha takwas, sai fiye da mutum dubu uku da ya rasa matsuguninsa.
  10. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace, shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wutar lantarki, ga tsadar taki, ga gadar da sukan samu su haura ta karye, gadar da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  11. Yanzun karfe hudu da minti takwas na asubah. Ana ruwan sama amma ba sosai ba. Zai bari mu je Sallar asubah kuwa?

Mu wayi gari lafiya.

Af! Har na tuna shekarar dubu biyu da goma sha biyu da Jonathan ya kara kudin man fetur, kowa ya fito yi masa zanga-zangar sai ya rage. Har wasu ke batun a kwace kasar a hannunsa saboda zargin ba shi da imani, ba ya tausayin talakan da ya za be shi. Haka kasar ta tsaya cik.

To na yi nan.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply