Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar ashirin da uku ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha biyu ga watan Satumba, na shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 188 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 47
Inugu 25
Filato 21
Abuja 14
Delta 10
Abiya 11
Bauci 8
Ondo 8
Kaduna 8
Ogun 6
Imo 5
Binuwai 4
Katsina 4
Taraba 4
Edo 3
Kwara 3
Oyo 3
Ribaa 2
Yobe 2

Jimillar da suka harbu 56,017
Jimillar da suka warke 43,993
Jimillar da ke jinya 10,942
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,076

 1. Gwamnatin Tarayya na nan tana shirin raba wa ma’aikatan sufuri wata naira biliyan goma kyauta a matsayin kudin tallafi na kwaronabairos.
 2. Nijeriya ta wuce kasar Indiya, har ta mata fintinkau bangaren masu samun waje a titi ba sakayawa su kantara kashi ba kunya ba tsoro.
 3. Ranar litinin mai zuwa wasu ‘yan makarantar firamare a jihar Neja za su koma makaranta.
 4. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci Babban Bankin Nijeriya, da kada ya kara ba wani kud da sunan zai shigo da kayan abinci ko taki kasar nan.
 5. Al’umomi a kalla dari ambaliyar ruwa ta durkusar a jihar Neja a daminar bana.
 6. Mailafiya ya bukaci kotu ta umarci ‘yan sanda su tsahirta yawan tambayoyin da suke damunsa da su. Karo na uku ke nan hukumar DSS na bukatar Mailafiya ya je tana nemansa.
 7. Masu yin burodin saidawa na shirin kara kudin burodi, saboda tsadar kayan hada burodin.
 8. A watan Disamba na shekarar nan za a gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Gwambe.
 9. Karon farko bayan shekara shida, an gudanar da jarabawar hukumar shirya jarabawa ta yammacin Afirka WAEC a Chibok.
 10. Wasu bayanai na nuna duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin Hausawa da Fulani da Atyap, an kashe wasu mutum biyu a yankin na Zangon Kataf na jihar Kaduna. Sai dai a hira da tashar TVC wani bafulatani Yandeh ya ce ba a kashe kowa ba. In ma an kashe to su ma fulani an kashe musu mutum hudu amma duk ana kokarin a ga an zauna lafiya ne.
 11. Mutanen Tungan Maje da ke yankin Abuja da kidinafas suka je suka musu kidinafin jama’a na can suna ci gaba da jimami.
 12. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba wutar lantarki. Akwai biyan karin kudin zama a duhu ke nan. Sai tsadar taki, ga gadar da sukan samu su haura ta karye, da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan suka zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi ga wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
 13. Kungiyar Daliban Nijeriya ta nemi Gwamnatin Tarayya ta janye karin kudin mai da na wuta da ta yi.
 14. Gwamna Ortom na jihar Binuwai ya bukaci sojoji su saki wadanda suka kama da Gana da aka kashe da ya ce tubabbu ne.
 15. Mutane dubu arba’in da bakwai suka nemi aikin rundunar tsaro ta Amotekun da ake neman mutum dubu biyu kawai a jihar Oyo.
 16. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi. Wasu malaman jami’o’i ma sun ce watan su uku ke nan ba albashi.
 17. Masu kamfanoni da masana’antun sun ce a shekarar dubu biyu da sha tara, sun kashe fiye da naira biliyan sittin da uku wajen samar wa kansu lantarki saboda gazawar kamfanonin lantarki wajen ba su wadatacciyar wutar.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Allah Ka raba mu da wanda kuke tare da shi kullum, wanda babban burinsa shi ne ya maka kazafi Amin.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply