Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, ashirin da daya ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma ga watan Satumba, shekarar dubu biyu da ashirin.
- Zuwa asubah da nake wannan rubutu, akwai sabbin harbuwa da kwarobairos 176 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Abuja 40
Legas 34
Filato 26
Inugu 15
Delta 12
Ogun 12
Ondo 9
Oyo 8
Ekiti 6
Ebonyi 4
Adamawa 2
Nasarawa 2
Kwara 2
Ribas 2
Edo 1
Oshun 1
Bauci 1
Jimillar da suka harbu 54,632
Nimiillar da suka warke 43,610
Jimillar wadanda suka riga mu gidan gaskiya 1070
Na ba da jingar a nemo jimillar wadanda ke jinya.
- Da yake na fara da batun kwaronabairos, akwai labarin da na ga yana ta karakaina a soshiyal midiya cewa gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna yana kashe naira dubu dari hudu wajen jinyar kowanne mai lalurar kwaronabairos.
- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani tsari na raba ‘yan Nijeriya su daruruwan miliyoyi da fatara, nan da shekara ta dubu biyu da talatin, da zai kare a shekarar dubu biyu da hamsin wato Nigeria Agenda 2050.
- Majalisar Dinkin Duniya ta yi tayin tallafa wa duk jihar da ta amince da ‘yan gudun hijira.
- Mutum wajen dubu biyu da dari biyu da sittin da ambaliya ta jikkata a jihar Katsina, ya tsere jihar Gwambe neman mafaka.
- Gwamna Ortom na jihar Binuwai ya bukaci sojoji su masa bayanin kisan da suka yi wa fitaccen makashin nan GANA.
- A wata shida, kwamitin nan na rabon kudaden da ake samu duk wata a raba FAAC, ya raba wa gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi naira tiriliyan uku.
- Gwamnatin Tarayya da likitoci da suka fara yajin aiki sun cimma matsaya a tattaunawar da suke yi. Har gwamnati ta ce ta biya ma’aikatan lafiya naira biliyan ashirin alawus na kwaronabairos, kuma yanzun haka shugaban kasa ya amince da wata naira biliyan kusan tara don biyansu abin da ya yi saura.
- Ma’aikatan lantarki sun yi bore a shalkwatar kamfanin raba wutar lantarki da ke Fatakwal.
- An nada Sarkin Kano Bayero a matsayin Shugaban Majalisar Sarakuna ta jihar Kano na dindindin. A da jujjuya shugabancin ake yi tsakanin sarakunan jihar.
- ECOWAS ta dakatar da aiki da kudi iri daya a tsakanin kasashen da ke cikin kungiyar, ta ce sai a hankali za ta aiwatar da wannan tsari.
- Hukumar da ke kula da kayyade farashin mai ta ce a yanzun aikinta ya kare tunda gwamnatin tarayya ta janye duk wani tallafi da take yi wa man fetur, ta kyale sai yadda kasuwar mai ta kaya a duniya.
- Wani shaida a shari’ar da ake yi wa tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya Mohammed Adoke, ya ce shi aka ba wata naira biliyan biyu ya canza ta zuwa Dala.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na korafin shekara daya da wata shida ke nan suna zaman dakon ariyas na sabon albashi.
- Malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya, na korafin wasunsu rabonsu da albashi wata uku.
- Mutanen kauyen Guibi da ke karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba a kawo musu wutar lantarki. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zsbe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Kayan abinci na ci gaba da tashin gwauron zabi, haka nan komai na ci gaba da tsada. Sai dai shi manomi kakarsa ce ta yanke saka. Dariya har kunne.
Mu wayi gari lafiya.
Af! Jiya bayan sallar la’asar na duka a kofar gida ina tuge ciyayi, da yake wani ya zo ya ari fatanyar da nake da ita, ta bace an ma rasa wa ya zo ya ara. Fatanya wajen ta goma aka ara duk sun bace wajen aro. Na duka ina tuge ciyayin sai ga wani ya zo ya ce “Yi hakuri ina zan samu SIGA?” (TABA SIGARI yake nufi).
Na mike na kalle shi na ce “Ni kake tambaya ina za ka samu siga?” Sai ya ce “Ai don Allah na ce” Yana yi yana kallon aljihuna ko ina da wata da na sha na rage in mika masa ko in nuna masa inda ake sayarwa. Sai Malam Umar Mainama da ke kusa yana kallonmu ya kuma ji me yake tambaya, ya tsomo baki ya ce masa “Kai ba lebura ba ne mai gidan ne” Sai ya ba da hakuri ya bazama neman taba sigari. Nan su KB da ke kusa ke cewa ba fa laifinsa ba ne. Shi lebura ne ya zo Kinkinau yana wani aikin, shi ne ya fito neman sigari, ya ga dan uwa lebura ya duka yana irin aikinsa, aikin da sai an hada da taba sigare, ko daya yayar tata wuiwui ko an afa daya abokiyar aikin wato kwaya, kafin a dukufa irin wannan aiki da ya ga ina yi. Sai na fashe da dariya, na duka na ci gaba da aikina. Can ma na ji wani na cewa na cika son kudin tsiya. Maimakon in kira wani in ba shi naira dubu daya ya nome, ni na je ina yi ga shi nan wani na mun daukar lebura mashayin sigari ko busata. Ni kuma nake cewa a zuciyata ‘wadannan mutanen ba su san ni ba ne’
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.