Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, goma sha tara ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da takwas ga watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 155 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 42
Filato 25
Ribas 16
Ebonyi 10
Abiya 9
Abuja 9
Ogun 9
Katsina 6
Kaduna 6
Ekiti 4
Taraba 4
Edo 3
Anambara2
Akwa Ibom 2
Kano 1

Jimillar da suka harbu zuwa yanzun 55,160
Jimillar da suka warke 43,231
Jimillar da ke jinya 10,868
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,061

  1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana kasar Nijar yana halartar taron kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS, har ya bai wa shugabannin kasashen da ke cikin kungiyar shawarar a guje wa kara tsawon wa’adin mulki da wasunsu ke yi ko yunkurin yi. Wato shugaban kasa ya yi wa’adin farko, ya yi na biyu, ya ce kuma sai ya yi tazarce, ya yi mulki karo na uku.
  2. Gwamnatin Tarayya ta ce kara kudin wutar lantarki da kudin fetur da ta yi, zai bunkasa tattalin arzikin kasar nan ba wani haifi.
  3. Gwamnatin Tarayya ta ce tunda ta kara kudin mai da na lantarki, za ta sanya ido don tabbatar da masu wuta da man ba sa damfarar talaka.
  4. Likitoci masu kokarin kwarewa sun soma yajin aiki jiya, sai dai minista Ngige ya nemi a dare teburin tattaunawa. Likitocin sun ce sun gaji da gafara sa ba su ga kaho ba ne.
  5. Su ma malaman kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na korafin sun soma gajiya da gafara sa ba su ga kaho ba, shekararsu daya da wata shida, suna dakon ariyas na sabon albashi har yau shiru.
  6. Babban Lauyan Gwamatin Tarayya kuma Ministan Shari’a Malami, ya ce tabbas za a hukunta wadanda suka taimaka aka damfari Nijeriya a kwangilar nan ta P&ID.
  7. Ibrahim Magu ya nemi a yi sammacin Malami zuwa gaban kwamitin da ke bincikarsa don bin bahasin wasu maganganu da yake zargin Malami ya yi a kansa da ba gaskiya ba ne.
  8. Dakarun soja sun kashe wasu ‘yan bindiga da ke addabar jihar Binuwai da ta Nasarawa.
  9. Ministan Labaru Lai Mohammed ya ce duk da karin kudin mai da aka yi, har yanzun man da dan Nijeriya ke sha ne ya fi arha.
  10. Gwamnatin Tarayya ta ce ta yi asarar kashi sittin cikin dari na yawan kudaden shiga da take samu saboda kwaronabairos.
  11. Gwamnatin Tarayya ta agaza wa wadanda ambaliya ta shafa, da kuma kungiyar Boko Haram ta shafa da kayan agaji.
  12. Wani bayani na nuna a duk wata ana kashe wa ‘yan gudun hijira wajen naira biliyan biyar.
  13. An kai Keita tsohon shugaban kasar Mali Daular Larabawa jinya, sai dai wasu bayanai na nuna sojojin da suka masa juyin mulki na cewa sun ba shi wata uku ya gama jinyar a can, ya koma gida.
  14. Shugaban kasar Ghana Nana ne ya zama sabon shugaban kungiyar ECOWAS.
  15. Mutanen kauyen Guibi, da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba wutar lantarki. Ga tsadar taki. Gadar da sukan samu su haura ta balle. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af? Jiya bakwai ga watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin, muka cika shekara ashirin da takwas da uwargida. An yi auren ranar bakwai ga watan Satumba na shekarar alif da dari tara da casa’in da biyu 7/9/1992, makona daya da dawowa daga bautar kasa NYSC daga Anaca a lokacin. An daura auren a ‘Yan Tukwane da ke Zango, a Tudun Wadar Kaduna, muka tare a layin Rock Rad da ke Tudun Nufawar Kaduna.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2697274940544900&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply