Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, goma sha takwas ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da bakwai ga watan Satumba, shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Zuwa asubahin nan akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 100 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 29
Abuja 22
Kaduna 19
Oyo 7
Ebonyi 6
Edo 3
Katsina 1
Ekiti 1
Bauci 1
Nasarawa 1

Jimillar da suka harbu 55,003
Jimillar da suka warke 43,013
Jimillar da ke jinya 10,938
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,057

  1. A yau litinin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Nijar taron kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka da za a yi karo na hamsin da bakwai.
  2. Gwamnatin Tarayya ta fitar da bayani dalla-dalla yadda ta yi da wata naira biliyan talatin da rabi da ‘yan kai a watanni hudu daga kudin tallafi da kuma yaki da kwaronabairos kamar yadda kungiyar SERAP ta nemi bahasi.
  3. Wata sanarwa daga shugaban hukumar kwastam na ankarar da mutanen Abuja da kewaye wani shiri da aka ce an bankado da kungiyar Boko Haram ta yi na kai hare-hare wasu yankuna na Abujan. Sannan wata sanarwa daga sojojin Nijeriya na watsi da duk wani tsoro ko fargaba a kan wannan batu.
  4. ‘yan sanda sun damke wasu ‘yan Nijeriya biyu da suka damfari wata jiha ta kasar Jamus, yuro miliyan goma da rabi da ‘yan kai da sunan kwaronabairos.
  5. Ingila za ta ba Nijeriya tallafi na bincike a kan kwaronabairos.
  6. Gwamnatin tarayya za ta bullo da amfani da jirgin sama wajen jefa ko wurga kayan tallafi ga al’umomi da ke wuraren da ke da wuyar kaiwa ko kutsawa.
  7. ‘yan bindiga sun kashe mutum takwas a kananan hukumomi guda biyar na jihar Kaduna.
  8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
  9. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace, shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wutar lantarki, ga tsadar taki, gadar da mutanen kan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Akwai bukatar jami’an tsaro su kara himma wajen tsaurara tsaro a hanyar Kaduna zuwa Abuja, musamman wuraren Katari. Don wasu bayanai na nuna kidinafas sun dawo wuraren suna cin karensu babu babbaka.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2696339163971811&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta