Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, goma sha bakwai ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da shida ga watan Satumba, shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Zuwa asubahin nan akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 162 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 53
Gwambe 21
Oyo 19
Delta 12
Ondo 11
Filato 10
Ebonyi 9
Abuja 6
Kwara 6
Kaduna 5
Ribas 3
Ogun 2
Anambara 2
Imo 2
Ekiti 1

Jimillar da suka harbu 54,905
Jimillar da suka warke 42,922
Jimillar da ke jinya 10,929
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,054

  1. A Nijeriya gabadaya zuwa yanzun an yi wa mutum dubu dari hudu da ashirin gwajin cutar kwaronabairos, inda aka gano mutum dubu hamsin da hudu da dari tara da biyar sun harbu, a cikinsu dubu arba’in da dari tara da ashirin da biyu sun warke, sai dubu goma, da dari tara da ashirin da tara da ke jinya, sai mutum dubu daya, da hamsin da hudu da ya riga mu gidan gaskiya.
  2. Jiragen kasashen duniya sun dawo da sauka a Nijeriya bayan kusan wata shida da dakatar da hakan saboda kwaronabairos, sai dai Nijeriya ta sa ka’idar kada jirgi daya da zai sauka kasar nan, ya sauka da fasinja fiye da dari biyu, amma idan zai fita daga Nijeriya zai iya dibar yawan mutanen ko fasinjan da yake so.
  3. Kungiyoyin jama’a daban-daban a jihar Oshun sun soma zanga-zangar kin amincewa da karin kudin lantarki da na mai.
  4. Shekaranjiya sai ga bayanin kidinafas a nan Kaduna sun tare hanyar Abuja jama’a masu ababen hawa an yi cirko-cirko. Jiya na ga bayanin da ke cewa jami’an tsaro sun dakile kokarin kidinafas din.
  5. Gwamnan jihar Binuwai Ortom ya bai wa duk wani mutum da ke zaune a arewa maso gabashin jihar da ya san ya mallaki makami, nan da zuwa jibi talata ya hanzarta mika shi don a yafe masa laifin da ya aikata a baya.
  6. Manoman shinkafa da ke jihar Sakkwato da Kabbi, sun yi asarar kudin da suka kashe a gonarsu ta shinkafa naira biliyan daya sakamakon ambaliyar ruwa da ta musu barna a gonakin.
  7. Jami’an tsaro sun ce sun dakile kidinafin har guda hamsin da hudu a watanni biyu da suka gabata.
  8. Ana ci gaba da korafi a kan yadda ake ta kara kudin samun damar kallo ta DSTV da dangoginsu.
  9. Malaman jami’a sun ce ba za su janye yajin aikin da suke kai ba, malaman kwalejojin ilimi na shirin zuwa yajin aiki, su kuma ma’aikatan kwalejojin foliteknik na ci gaba da dakon ariyas, da suka yi shekara daya da wata shida suna jira.
  10. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da kasancewa a killace saboda shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wuta, ga tsadar taki, ga gadar da sukan samu su haura ta karye, da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa har yau shiru bai gyara musu ba.
  11. An daura auren diyar shugaban kasa Muhamnadu Buhari mai suna Hanna Buhari da angonta Mohammed Turad shekaranjiya.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Wani ke tambayata kamar ya taba ganina ina labaru da gidan talabijin na kasa NTA Kaduna wasu shekaru can baya. To tabbas na yi aiki da NTA wato fassara Taskar Labaru a NTA a shekarar 1995. Kafin nan ina aiki da rediyon jihar Kaduna a 1994. Da aka bude gidan talabijin na jihar Kaduna wato KSTV a shekarar 1996, ni ne mutum na farko da na soma karanta labaru a tashar. Esther Tachio ta soma karanta labarun turanci. Daga nan na je NewAge na shekara daya a matsayin mai horas da su aikin jarida da Hausa. Da ya sa na zama mai horaswa, har na zaga NTA, da FRCN, da KSMC, da Nagarta, da Liberty, da Freedom, da KASU FM, da Kaduna Media Academy, da DITV/Alheri Rediyo, da daliban Mass Communication na kwalejin foliteknik ta Kaduna, na kuma rike gidan rediyon sifaida na kwalejin foliteknik na dan wani lokaci, daga bisani aka nada ni manajan shirye-shirye na rediyon na zuwa karshen watan da ya gabata na Agusta. A yanzun haka ina tallafa wa ma’aikatan dakin labaru na DITV/Alheri rediyo da ke Kaduna. Kada a manta ni lakcara ne a sashen harsuna na kwalejin foliteknik ta gwamnatin tarayya da ke Tudun Wadar Kaduna kuma duk digirorina a Hausa ne wato Hausa na karanta. Na dade ina yi wa jaridar Leadership Hausa da Mujallar Muryar Arewa rubutu, na kuma yi babban editan mujallar JUNIOR SPIDER na tsawon shekara biyar. Na taba koyarwa a Labayi ta Unguwar Mu’azu Kaduna a 1992, da kwalejin Trinity da ke Barnawa a 1996 sai Kaduna Polytechnic Demonstration Secondary School, da makarantar Joy international, da makarantar FGGC Onitsha a 1991 da na je bautar kasa Anaca. Na kuma koyar tare da shugabantar sashe a SPRS (School of Preliminary and Remedial Studies) ta kwalejin foliteknik ta Kaduna.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2695507130721681&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Exit mobile version