Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, goma sha shida ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da biyar ga watan Satumba, shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 156 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 36
Abuja 35
Oyo 29
Kaduna 10
Abiya 9
Oshun 5
Ogun 5
Inugu 5
Ribas 4
Nasarawa 3
Ekiti 3
Imo 3
Edo 2
Kwara 2
Katsina 2
Filato 2
Neja 2

Jimillar da suka harbu 54,743
Jimillar da suka warke 42,816
Jimillar da ke jinya 10,876
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,051

  1. Jiya na sayi mai a gidajen mai guda biyu, kowanne yana sayar da kowacce lita naira dari da sittin. Lita goma dubu daya da dari shida. Lita goma na sha. Haka na sha, a baifas, na je titin Ahmadu Bello, na koma Kinkinau, na je rediyon Libati, na je aiki talabijin na DITV da alheri rediyo, na dawo gida, man ya tafi ta sona nuna ta shiga danja. Da zan dawo gida ne na bi wani gidan man na saya a galan na janareta don haka muka yini jiya ba wuta, sai cikin dare suka dawo da ita.
  2. Kofin shayi da siga da liftan ba madara, da ake sayarwa naira talatin, a yanzun ya zama naira hamsin. Kwai guda biyu a wajen mai shayi da in an soya naira dari ne, a yanzun naira dari da ashirin ne. Indomi da ake sayarwa naira dari, yanzun dari da ashirin ne. Kwalbar man gyada, da ake sayarwa naira dari hudu da arba’in, yanzun naira dari biyar ce. Sai su shinkafa da masara da dawa da kowa ya san yadda suka yi tashin gwauron zabi.
  3. Kungiyoyi da daidaikun jama’a ciki har da kungiyoyin kwadago, na ta cewa gaskiya karin kudin mai da na wuta da aka yi, zai shafi farashin komai a kasuwa.
  4. Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya bai wa shugaban majalisar wakilai Gbajabiamila da ya yi tattaki zuwa Ghana a kan cin zarafin da ake yi wa ‘yan kasuwa ‘yan Nijeriya, tabbacin cewa za su sake tunani a kan dala miliyan daya jalin da suka ce dole sai kowanne dan kasuwa dan Nijeriya ya mallaka kamar yadda yake a dokar kasarsu.
  5. Kungiyoyin kawance na Arewacin kasar nan, sun bukaci ko shugaban kasa ya janye karin kudin mai da na wuta, ko su bijire masa da karfi da yaji.
  6. Shugaban kasa Muhamnadu Buhari ya bukaci hukumar kula da agajin gaugawa ta kasa NEMA da ta agaza wa wadanda ambaliya ta yi wa barna a jihar Jigawa.
  7. Likitoci da aka fi sani da RESIDENT DOCTORS za su fara yajin aiki daga ranar litinin mai zuwa.
  8. Malaman da ke koyarwa a kwalejojin ilimi na gwamnatin tarayya za su soma yajin aiki.
  9. Malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya da ke yajin aiki, sun ce babu ranar janye yajin aikin. Sun kuma ce ba a tausaya wa talaka ba da aka kara masa kudin wuta da na mai alhali yana cikin wani mawuyacin hali.
  10. Kotun Ingila ta jinjina wa Ibrahim Magu da hukumarsa ta EFCC saboda iya bankado damfarar da aka yi a batun P&ID, har kotun a jiya ta daga wa Nijeriya kafa ta ba ta isasshen lokaci ta daukaka kara a kan tararta da ta ci dala biliyan goma.
  11. Sojojin Sama sun kai farmaki wani daji na Kaduna suka kashe ‘yan bindiga da dama a muhallinsu da ke dajin.
  12. Jakadan kasar Rasha a Nijeriya Alexey Shebarshi ya mika wa ministan lafiya na Nijeriya Osagie wani maganin kwaronabairos da Rasha ta hada. Shi ministan ya mika wa hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC don duba ingancinsa.
  13. Malaman kwalejojin fokiteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
  14. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace, shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wuta. Ga tsadar taki. Ga gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! A rana mai kamar ta jiya hudu ga watan Satumba na shekarar dubu biyu da goma sha hudu wato 4/9/2014, shekara shida ke nan na yi wannan rubutun da ke biye:

‘Da yake na ji Ahmed Maiyaki babban Daraktan yada labaru na Ramalan Yero yana mayarwa da Yaro Makama Rigachikun martani a shirin kowanne gauta cewa rikicin tsufa ke damun Yaro Makama saboda Ramalan Yero ya malala kwalta har kofar gidan Yaro Makama. Da jin haka na niki gari na tafi Rigachikun na ga kwaltar. To mu Kinkinau laifin me muka yi? Idan ka biyo ta sabuwar Fanteka zuwa Nasarawa, kwalta ta shiga Kurmin Mashi, wata ta shiga Hayin Dan Mani, wata ta shiga Rigasa, wata Hayin Malam Bello, wata ta shiga Kabala, wata ta yi Zango, wata Unguwar Mu’azu wata ta shiga Dirkaniya,wata ta shiga Nasarawa. Mu Kinkinau fa?’

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2694635380808856&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply