Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, ashirin da daya ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha uku ga watan Yuli, na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Wani rahoto na Bibisi Hausa na cewa sojojin Nijeriya su wajen dari uku da hamsin ke shirin fita daga aikin sojan a watan Janairu na shekarar dubu biyu da ashirin da daya, saboda wasu dalilai har da na rashin isassun kayan aiki.
  2. Shugabannin Majalisun Dokoki na jihohin Arewa goma sha tara, sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi hobbasa domin magance matsalar tsaro da ta kwaronabairos da ke hauhawa kullum a jihohin Arewa.
  3. Kungiyar SERAP ta kare hakkin bil’Adama, ta nemi kotu ta tilasta wa gwamnonin kasar nan talatin da shida, amfani da makudan kudaden da ake ba su da sunan tsaro SECURITY VOTES, da kudaden fansho da ake biyan wasu tsofaffin gwamnoni, wajen samar da kayayyakin kula da lafiya da yakar kwaronabairos.
  4. Kudaden rara na danyen manfetur na Nijeriya sun kai dala miliyan 72.14, fiye da dala miliyan 71.81 da Nijeriya ke da su a watan Maris na shekarar nan.
  5. Sojojin sama na Nijeriya sun kai farmaki wani daji na jihar Zamfara da mafakar ‘yan bindiga take.
  6. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata uku suna zaman jiran ariyas na sabon albashi.
  7. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su dari uku da saba’in da daya a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 152
Ebonyi 108
Edo 53
Ondo 46
Abuja 38
Oyo 20
Kwara 19
Filato 17
Oshun 14
Bayelsa 14
Ekiti 14
Katsina 14
Akwa Ibom 11
Kaduna 11
Ribas 11
Neja 10
Ogun 7
Kano 6
Kuros Ribas 4
Bauci 2

  • Kaduna 11, Kano 6 !

Jimilar wadanda suka harbu 32,558
Jimillar wadanda suka warke 13,447
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 740
Wadanda ke jinya 18,371

Mu wayi gari lafiya.

Af! Allah Ka raba mu da sharrin mutum amin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply