Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, goma sha hudu ga watan Muharram shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da uku ga watan Satumba, shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Talakan Nijeriya na korafin yana kukan targade sai ga karaya ta auku. Yana kukan an kara masa kudin lantarki sai ga karin kudin man fetur zuwa kusan naira dari da hamsin da biyu kowacce lita. Ga man da ma masu ababen hawa na korafin da an zuba maka, sai ka ga ya bi iska wayam. Ga zaluncin tauye mudu na masu man, shi kuna lantarkin aka masa karin kudin zama a duhu.
 2. Kungiyar Masu Sarrafa Kaya ta Nijeriya wato Manufacturers Association of Nigeria MAN ta soki karin kudin wutar lantarkin da aka yi, da bayanin cewa dole komai zai yi tsada. Karin na nuna iya-kudinka-iya-shagalinka.
 3. Talaka na korafin daga sanar da karin kudin man, masu gidajen mai ba su jira man da ke hannunsu da suka saya ya kare ba, suka murda famfonsu zuwa karin. Talaka ya ce da rage kudin aka yi, da ba su yi saurin gyara litar tasu ba.
 4. Talakawa da aka zanta da su a kan karin kudin wuta da na mai, ga tsadar kayan abinci, sun ce a tunawa Baba Buhari ba alkawarin da ya musu a lokacin yakin neman zabe ba ke nan.
 5. Malaman jami’o’i sun ce ba fa za su koma aiki ba, muddin gwamnatin tarayya ba ta biya musu bukatunsu ba.
 6. Gwamnatin tarayya ta ce za ta sanya wutar lantarki a gidaje guda miliyan biyar da ke karkara da wata naira tiriliyan biyu da kusan rabi wato 2.3 Trillion Naira.
 7. Masu kiwon kaji da sauran ‘yan tsaki na korafi a kan karacin masara tare da kiran a agaza musu.
 8. Tukur Buratai ya agaza wa wani tsohon soja Paul Ojo mai shekara tamanin da biyar a duniya, da gida mai tsarin dakuna uku, a Kaduna, bayan an masa wulakanci har da mangari, a lokacin korarsu shi da wasu daga wasu gidaje a Kaduna. Tsohon soja ne waran ofisa.
 9. ‘Yan sanda biyu suka riga mu gidan gaskiya a lokacin da wani hadarin mota ya auku a ayarin Oshiomhole da ke yawon yakin neman zabe na jihar Edo.
 10. Gwamnatin Tarayya ta amince za ta kashe naira tiriliyan uku da ‘yan kai wajen sabunta aikin tara kudaden shiga na hukumar kwastam, don ta iya tara ninkin ba ninkin kudin shigan da take tarawa a yanzun.
 11. Kungiyar Kiristoci ta Kasa ta rubuta wa shugaban kasa wasikar neman ya dakatar da sabuwar dokar nan da ta shafi kamfanoni da dangoginsu CAMA 2020 da ya sa wa hannu kwanakin baya, da kungiyar ke ta korafin shedaniyar doka ce da za ta durkusar musu da coci.
 12. Ambaliyar ruwa na ci gaba da barnata gonaki, da amfanin gonaki, da muhalli da sauransu, a jihar Kaduna da jihar Katsina da wasu sassan kasar nan.
 13. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
 14. An kwantar da Keita na kasar Mali a asibiti yana jinya, bayan sojojin da suka masa juyin mulki sun sako shi daga inda suke tsare da shi.
 15. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace, shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wuta, ga tsadar taki, ga gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan suka zabe shi zai gyara musu. Sun yi nasa sun zabe shi, ga wa’adinsa na shirin karewa bai yi nasa ya gyara musu ba.
 16. Ga wadanda ke iya ganin hoto a rubutuna, hoton da ke biye garin masara ne nikakke kwatan buhu da na sayo jiya da almuru. Naira dubu shida. Bai kai mako daya da na ce na sayo kwatan naira dubu biyar da dari bakwai da naira hamsin ba. Da ke nuna buhun garin a yanzun sai kana da naira dubu ashirin da hudu. Buhun da nake saye a can baya naira dubu takwas. Da azumin da ya gabata kwatan ya kai naira dubu uku da dari biyar. Yanzun naira dubu shida ne kwatan. Ba mu san nan da karshen wata nawa zai kai ba.
 17. Yanzun karfe hudu na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 216 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Filato 59
Ribas 27
Abiya 22
Legas 20
Oyo 18
Inugu 17
Kaduna 11
Abuja 11
Ogun 10
Ebonyi 4
Oshun 4
Ekiti 4
Delta 3
Edo 3
Akwa Ibom 2
Bauci 1

Jimillar da suka harbu 54,463
Jimillar da suka warke 42,439
Jimillar da suke jinya 10,997
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,027

Mu wayi gari lafiya.

Af! Idan an lura jiya labaru falan biyu na rubuta. Na yi na farko na sake shi na ga ya bace. Na neme shi na rasa ya yi batar dabo ko in ce layar zana. Shi ne na sake rubuta wani sabo a lokacin. Ina sakin sabon sai ga tsohon da sabon sun bayyana har jama’a wasu sun soma tsokaci a na farkon wasu a na biyun. Sai na bar su biyun da fatan na yau ba zai yi layar zana daga bisani ya bayyana ba.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply