Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalanu alaikum barkanmu da asubahin laraba, goma sha uku ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da biyu ga watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Daga jiya talakan Nijeriya zai fara biyan sabon kudin zama a duhu musamman a jihar Kaduna da Abuja.
  2. Sanatoci sun musanta an ba kowannensu naira miliyan ashirin, kowanne dan majalisar wakilai naira miliyan goma sha biyar, daga hukumar kula da raya yankin Neja Delta, da sunan tallafi na kwaronabairis. An kuma ji wani Ojugbe na cewa da za a wallafa sunayen gafiyoyin da suka wawuri kudade daga hukumar, da kasar nan ta balle.
  3. Yau Shugaban Majalisar Wakilai Gbajabiamila zai yi tattaki zuwa kasar Ghana don ganawa da shugaban majalisar dokoki na kasar ta Ghana, a kan duka da tsinka jaka da takalmi da ake yi wa ‘yan kasuwan Nijeriya da ke can.
  4. Da yake gwamnoni musamman na kasashen yarbawa na ta sanar da ranakun bude makarantunsu manya da kanana, kwamitin shugaban kasa a kan kwaronabairos ya ce a dai yi hattara.
  5. Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum hamsin a jihar Neja, dubbai suka rasa muhallansu.
  6. A jihar Kabbi wani kwale-kwale ya kife da wasu mata da yara, da yawancinsu suka riga mu gidan gaskiya.
  7. Gwamna Ishaku na jihar Taraba, ya hori Tibawa wato Munci, da Jukunawa su zauna lafiya da juna.
  8. Sojoji sun ceto wasu mutum goma da aka yi kidinafin a jihar Katsina.
  9. Wasu likitoci a Abuja sun sona yajin aiki saboda sun ce har yanzun ba su shaida ba, batun alawus na kwaronabairos.
  10. Iran ta ce Hadaddiyar Daular Larabawa ta ba kasashen musulmi kunya da har da kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Izira’ila, har ta amince jirgin Izira’ilan ya sauka a daular.
  11. Manoman Nijeriya da suka noma shinkafa da masara a bana, suna ta murnar kakarsu ta yanke saka, saboda abin da suka noma suna kudi.
  12. Yanzun karfe hudu da minti shuda da wasu dakikoki na asubah. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 239 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Filato 116
Abuja 33
Legas 19
Ekiti 12
Kaduna 11
Ogun 11
Ebonyi 8
Binuwai 7
Abiya 5
Delta 5
Ondo 4
Edo 3
Imo 2
Oshun 2
Bauci 1

Jimillar da suka harbu 54,247
Jimilar da suka warke 42,010
Jimillar da ke jinya 11,214
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,023

Labarun ke nan sai kuma korafe-korafe kamar haka:

  1. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi har yau shiru.
  2. Mutanen Kinkinau da ke yankin karamar hukumar Kaduna ta Kudu, na ci gaba da korafin masu tallar maganin gargajiya a baro da manyan lasifikoki, na damunsu da tallar magani da batsa a unguwa ba kakkautawa.
  3. Talakan Nijeriya na ci gaba da korafin rayuwar ta yi tsada komai ya yi tashin gwauron zabi.
  4. ‘Yan Nijeriya sun soma korafi a kan karin kudin wutar lantarki.
  5. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba wuta. Ga tsadar taki. Ga gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe cewa idan suka zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba. Ga wadanda ke iya ganin hoto a rubutuna, ga hoton gadar nan a kasa lokacin ba ta karasa ballewa ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ga lambar wayar dan damfarar nan da ya mun kidinafin wasaf ya bi jama’ar da suke wasaf da ni yana damfararsu. 07082391996
Ina kuma sanar da jama’a a fice daga tsohon dandalina DANDALIN ISHAQ IDRIS GUIBI don yana hannun dan damfaran har da hotona ya sa, a koma sabon da na bude DANDALIN ISHAQ GUIBI

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply