Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, goma sha biyu ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W Daidai da daya ga watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Ina cikin yin wannan rubutu daidai karfe uku saura minti goma sha shida na dare aka tsuge da ruwan sama kamar da bakin kwarya. Ruwa ne kam mai karfin gaske.
 2. Talakan Nijeriya na cewa yana dandana kudarsa a bana saboda tsadar rayuwa musamman kayan abinci da sauran kayan abin masarufi.
 3. Manomin da ya noma shinkafa da masara a bana ya ce shi kakarsa ta yanke saka, yana ta darawa da shanawa, wasu na ta sayen motoci da sauransu saboda kayan da ya noma na daraja.
 4. Gwamnatin tarayya ta ce za ta zuba naira biliyan dari shida bangaren aikin gona.
 5. Mutanen Kinkinau da ke karamar hukumar Kaduna ta Kudu, na ci gaba da korafin wasu da ke yawo da maganin gargajiya a baro suna talla, na yawan damunsu da tallar batsa da lasifika.
 6. A yau za a rantsar da Akinwumi Adeshina a matsayin shugaban Bankin Raya Afirka, karo na biyu da zai yi shekara biyar yana jan zarensa.
 7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da gunagunin shekara daya da wata shida ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi har yau shiru.
 8. Kotun Koli ta yi fatali da karar da PDP da SDP suka kai gwamna Yahaya Bello da nake yi wa kirari da KWARONABAIROS KARYA CE a kan zabensa na gwamna, da tabbatar masa da kujerar da yake kai.
 9. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace, shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wuta, ga tsadar taki, gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe. Idan suka zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
 10. Ma’aikatan tashoshin jiragen sama sun yi zanga-zanga ta lumana, ta nuna ba su yarda da shirin da gwamnatin tarayya ke yi na jinginar da wasu manyan tashoshin kasar nan guda hudu ba.
 11. Ministan labaru na kasar Ghana ya mayar wa da ministan labaru na Nijeriya Lai Mohammed martani a kan zargin cin zarafin ‘yan Nijeriya da ke kasuwanci a Ghana, da aka tilastawa biyan dala miliyan daya kowanne dan kasuwa. Sai dai a martanin mai shafi shida, an gano Ghana na jin haushin rufe kan iyaka da Nijeriya ta yi ne tun bara, da ya sa kayayyakin da Ghana ke yi tana haurowa da su kasar nan, na can suna musu kwantai. Da ke durkusar da tattalin arzikinsu. Shi ne suke fanshewa a kan ‘yan kasuwan Nijeriya da ke can.
 12. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin sasanta rikicin cikin gida na APC da ya ce yana matukar ci masa tuwo a kwarya. Haka nan an kaddamar da wani kwamiti na kyautata fahimtar juna tsakanin bangaren zartaswa da na majalisa.
 13. Bangaren Majalisar Dokoki ya ce ba zai sake lamuntar wadanda shugaban kasa ya nada mukamai na kawo musu wargi ba.
 14. Wasu ‘yan Nijeriya na tambayar ina aka kwana ne batun tsaurin ido da ake zargin karamin ministan kwadago Keyamo, ya yi wa ‘yan majalisa, da kuma zargin da Akpabio ministan raya yankin Neja Delta ya yi wa ‘yan majalisa ne?
 15. Ana ci gaba da ankarar da talakan Nijeriya cewa shi ne yake hauma-haumar banza a kan shugabannin kasar nan, ya dauka kan su a rarrabe yake. Aka ce ya dai duba yadda Jonathan ya zama dan lele a fadar shugaban kasa.
 16. Hukumar shirya jarabawa ta kasa NECO za ta kammala rajistar masu jarabawarta ranar goma sha daya ga watan nan.
 17. Gwamnatin jihar Kano ta tantance kanawa su fiye da dubu bakwai daga kananan hukumomi ashirin da hudu na jihar don tura su a dauke su aikin dan sanda.
 18. Ranar ashirin da daya ga watan nan za a bude makarantu a jihar Oshun.
 19. Ranar ashirin da shida ga watan nan za a mayar da mutanen garin Baga da ke jihar Barno, da kungiyar Boko Haram ta tarwatsa, gidajensu.
 20. Yanzun karfe hudu da minti goma na asubah. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 143, sabanin jiya da ake da 138. Ga alkaluman da jihohin:

Filato 35
Kaduna 21
Legas 19
Abuja 13
Ebonyi 9
Adamawa 7
Inugu 7
Katsina 7
Edo 6
Kwara 5
Oshun 3
Anambara 2
Kano 2
Neja 2
Ogun 2
Binuwai 1
Barno 1
Sakkwato 1

Jimillar da suka harbu 54,008
Jimillar da suka warke 41,638
Jimillar da ke jinya 11,357
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,013

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ga lambar wayar wanda ya mun kidinafin wasaf 07082391996. Kuma ina ci gaba da ankarar da wadanda har yanzun suke cikin tsohon dandalina na DANDALIN ISHAQ IDRIS GUIBI, Su fice daga cikinsa don yana hannun kidinafas na fesbuk da wasaf,, su dawo sabon da na bude wato DANDALIN ISHAQ GUIBI. A lura da bambancin sunan.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply