Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, goma sha daya ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da talatin da daya ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Yanzun karfe hudu na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 138 a jihohi da alkalumma kamar haka:

Filato 55
Legas 15
Ebonyi 11
Oyo 11
Abiya 8
Anambara 7
Abuja
Ribas 7
Kaduna 6
Ondo 5
Kwara 3
Bauci 1
Binuwai 1
Edo 1

Jimillar da suka harbu 53,865
Jimillar da suka warke 41,513
Jimillar da ke jinya 11,339
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,013

 1. Wasu likitoci a asibitin gwamnatin tarayya da ke Yola sun yi nasarar raba wasu ‘yan biyu ‘yan mako takwas Mercy da Grace da aka haifa manne da juna a jihar Bayelsa. Kyauta likitocin suka yi aikin, ana gama raba ‘yan biyun jirgin saman mayakan saman Nijeriya ya dauki ‘yan biyun da mahaifiyarsu zuwa gida Bayelsa, har gwamnatin tarayya ta yaba wa likitocin.
 2. Kungiyar Dattawan Arewa ta ce ba ta goyi bayan sake yi wa kundin tsarin mulkin kasar nan kwaskwarima a yanzun ba. Ta ce abin da ake bukata a Nijeriya a yanzun fiye da komai shi ne tsaro, da bunkasa tattalin arziki da sauransu.
 3. Daga yau an hana masu keke nafef bin titin da ya taso daga Kawo, har titin Ali Akilu zuwa titin Ahmadu Bello zuwa mahadar kwaman duk da ke cikin garin Kaduna. An kammala yi wa masu keken rajista, yau za a fara ta ‘yan bas don tabbatat da tsaro da kare lafiya masu keke nafef da ‘yan bas, da fasinjojin da suke dauka, kamar yadda gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana.
 4. Ana ci gaba da ankarar da masu mota da ke bin hanyar Kaduna zuwa Zariya, da su yi hattara saboda gadar da ke kusa da kasuwar duniya kafin Rigachikun ta bule, ta yi wagegen rami a tsakiyar titin.
 5. Gwamnatin kasar Ghana ta ce sam ita allambaran ba ta ci zarafin wani dan Nijeriya ba.
 6. Gwamnan jihar Zamfara na shirin yin dokar hukuncin kisa ga direbobin da suka yi tukin ganganci aka mutu.
 7. ‘Yan sintiri sun yi nasarar kashe kidinafas uku a Yobe bayan sun yi kidinafin wani a Damaturu.
 8. Wasu da ba a san ko su wane ne ba a masarautar Ham wato Jaba da ke jihar Kaduna, sun kashe wani dan bafulatani, abin da ya tayar da hankalin Fulani da Jaba don ba a irin wannan kai hari a masarautar. Har kwamishinan tsaro Aruwan tare da jami’an tsaro suka ziyarci yankin don ba iyayen dan bafulatanin hakuri, da tabbacin za a gudanar da bincike. Hantar mutanen yankin ta kadu saboda an san in ba a yi hankali ba, sai fulani sun mayar da biki.
 9. Wasu sun kashe kwamandan ‘yan JTF na Barnawa da ke cikin garin Kaduna Yahaya Adamu Danbaba.
 10. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya gargadi ‘yan siyasa a kan zaben jihar Edo da Ondo.
 11. Kungiyar kare hakkin jama’a SERAP a takaice, ta kai shugaban kasa Muhamnadu Buhari kotu, tana bukatar sai ya bayyana wa ‘yan Nijeriya, daga hannu su wa aka kwato wata naira biliyan dari takwas, da me aka yi da kudin, da shaida. Haka nan kungiyar na bukatar a binciki wata naira biliyan hamsin da daya da ake zargin wasu gafiyoyi sun kwashe a shekarar da ta gabata.
 12. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida suna dakon ariyas na sabon albashi har yau shiru.
 13. Yara ‘yan Islamiyya da iyayensu, na nan suna ci gaba da korafin sun gaji da zaman gida, haka nan su ma malaman nasu da masu makarantun.
 14. Talaka na ci gaba da korafin rayuwar ta yi tsada.
 15. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a kiillace, shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wuta, ga tsadar taki, ga gadar da sukan samu su haura ta balle. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe idan sun zabe shi zai gyara. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
 16. Ana nan ana ci ga da tir da cin mutuncin da Femi-Fani-Kayode da ke jin shi tsohon minista ne kuma lauya ya yi wa wani dan jarida. Kodayake ya dawo ya ce ya tuba.
 17. Manoman shinkafa da masara na nan suna darawa da shanawa saboda kayan amfanin gonan sun yi daraja a daminar bana.

Mu wayi gari lafiya.

Af! A rana mai kamar ta jiya 30 ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da goma sha uku 30/8/2013 na yi wannan rubutu da ke biye:

‘A yanzun haka kamfanin Guibi-Hausa Consultancy Services ya kammala fassara wani littafi mai suna Ante-Natal Care. A wancan makon da ya gabata ne kamfanin ya fassara The Cid of Baghdad. Wannan dama ce ga duk mai son a fassara masa littafi cikin sauki kuma ba bata lokaci cikin daidaitacciyar Hausa’

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply