Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, tara ga watan Muharam, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da tara ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.
- Shugaban kasa Muhamadu Buhari ya goyi bayan wa’adin shekara daya tal ba kari, da kungiyar ECOWAS ta raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ta ba sojojin da suka kwace mulki a Mali, su mayar da mulki ga farar hula ko su yaba wa aya zaki.
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa da faduwar da wani jirgi mai saukar ungulu ya yi jiya a Ikeja da ke Legas , har mutane ukun da ke cikinsa suka riga mu gidan gaskiya.
- Nijeriya ta gargadi kasar Ghana cewa shiru-shiru fa ba tsoro ba ne, cin kashin da take yi wa ‘yan Nijeriya ya fa isa haka nan. Nijeriya ta ce jin kunyar mara kunya asara ce lakuce hancin da Ghana ke ci gaba da yi wa ‘yan Nijeriya latsin ya isa haka don kuwa Nijeriya za ta maka Ghana a kotun ECOWAS.
- Sanata Ndume ya ce yana ji yana gani ba ya iya zuwa kauyensu Ambada da ke Gwoza saboda tsoron ‘yan kungiyar Boko Haram.
- Lauya Femi Falana ya rubuta wa Babban Bankin Nijeriya wata wasika, yana so bankin ya masa bayani filla-filla yadda ya raba wata naira biliyan dari uku da talatin da takwas da rabi da ‘yan kai, na asusun kwaronabairos.
- Mutanen kauyen Damisi da ke yankin karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, sun yi korafin cikin mako biyu an yi kidinafin mutanensu su goma sha biyar. Haka nan wani bayani na nuna an yi kidinafin dan sanda daya da sibildifensi daya a wurare Marabar Rido da ke wuraren. Sannan a kokarin yin kidinafin da bai yi nasara ba, kidinafas sun harbe mutum biyu sun riga mu gidan gaskiya duk a jihar ta Kaduna.
- Firaministan kasar Nijar ya kawo wa gwamnan jihar Zamfara Matawalle ziyara a kan yadda za a hada kai don magance ‘yan bindiga na kan iyaka.
- Masu ababen hawa na ci gaba da korafi a kan tsadar man fetur, da yadda ake tauye musu mudun mai idan sun je sayen mai a gidajen mai.
- Talaka na ci gaba da korafi a kan tsadar kayan abinci, sai dai manoma da suka noma shinkafa a bana, kakarsu ta yanke saka suna ta sayen motoci.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan, suna dakon ariyas na sabon albashi shiru.
- Majalisar Wakilai ta yi barazanar za ta kwace kwangilar titin Abuja zuwa Kano saboda tafiyar hawainiya da aikin ke ci gaba da yi.
- Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wutar lantarki, ga tsadar taki, ga gadar da sukan samu su haura ta balle, gadar da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan suka zabe shi, zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Yanzun karfe hudu da minti goma na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 160 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Filato 44
Legas 27
Katsina 18
Edo 15
Abuja 14
Ondo 10
Oyo 9
Kwara 6
Abiya 4
Nasarawa 4
Kano 3
Ekiti 2
Kaduna 2
Kabbi 1
Ogun 1
Jimillar da suka harbu 53,477
Jimillar da suka warke 41,017
Jimillar da ke jinya 11,449
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,011
Mu wayi gari lafiya.
Af! Dilin-dilin!
Dilin-dilin !!
Dilin-dilin !!!
Dilin-dilin!!!!
Dilin-dilin!!!!!
Wanda bai gane karatun ba to na samu rahoton ma’aikatan gwamnatin tarayya, har da wadanda aka saba musu jinkiri duk sun ga dilin-dilin wato albashi jiya.
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.