Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, takwas ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da takwas ga watan Agusta, shekarar dubu biyu da ashirin.
- Sojojin Nijeriya sun ayyana kungiyar Dar-Ul-Salam a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda, suka kuma ce ‘yan kungiyar yawanci mata da yara su wajen dubu uku da dari hudu da goma suka mika wa sojojin kai a karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa.
- Shugaban kasa Muhamnadu Buhari, da tsohon shugaban kasa Jonathan, sun taya Akinwumi Adeshina murnar sake zabarsa da aka yi a matsayin shugaban bankin raya Afirka, da zai sake yin wata shekara biyar yana jan ragamar kungiyar.
- Gwamnatin tarayya ta cire kudin fiton shigo da mitar wutar lantarki kasar nan na tsawon shekara daya, a burin shugaban kasa Buhari na tabbatar da an wadata ‘yan Nijeriya da mitar iya-kudinka-iya-shagalinka don daina cutar talaka da ke biyan kudin wutar da bai sha ba wato ESTIMATED BILLING.
- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Kanal Dikio mai ritaya a matsayin kantoman rikon shirin nan na ahuwa wato AMNESTY PROGRAMME, bayan ya fatattaki Dokubo da ake zargin dan damfara ne daga shugabancin shirin.
- Gwamnatin tarayya ta dage maido da zirga-zirgar jiragen sama na duniya kasar nan har sai biyar ga watan gobe.
- Hukumar tasoshin jiragen sama ta kasar nan FAAN ta kara kudin hidimar fasinja daga naira dubu daya zuwa naira dubu biyu.
- Kungiyar Jama’atu ta ce tana goyon bayan yunkurin da gwamnan jihar Kaduna El-Rufai ya yi na nemo tsofaffin rahotannin binciken da aka yi a can baya a kan rikicin kudancin jihar Kaduna don aiwatar da su.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wajen wata shida ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi har yau shiru.
- Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace, shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wuta, ga tsadar taki, ga gadar da sukan samu su haura ta karye, gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzu, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan suka zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Mali sun saki Boubacar Keita da suka yi wa juyin mulki daga inda suke tsare da shi.
- A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito an jima da safe don karanta shafukana da ke dauke da labarun da na kawo daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis.
- A duniya bakidaya mutum miliyan ashirin da hudu da dubu dari biyu ya harbu da kwaronabairos.
- A Nijeriya akwai sabbin harbuwa da kwarona su 296 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Filato 85
Inugu 46
Oyo 31
Lagos 21
Ribas 20
Abuja 15
Kaduna 13
Bauci 12
Delta 11
Ekiti 11
Akwa Ibom 7
Ebonyi 6
Kwara 5
Ogun 4
Oshun 4
Gwambe 3
Neja 2
Jimillar da suka harbu 53,317
Jimillar da suka warke, 40,726
Jimillar da ke jinya 11,580
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,011
Mu yi juma’a lafiya.
Af a rana mai kamar ta yau, shekara shida daidai yau wato 28/8/2014 na yi wannan rubutun kamar haka:
‘Ina sauraron Rediyon Freedom/Firidom a yanzun haka, ana kiran waya ana ba da gudunmawa, sai dai duk wanda ya kira sai ka ji kuwwa, sai masu gabatar da shirin su ce wa wanda ya kira ya matsa kusa da akwatin rediyonsa don maganin kuwwar. Ba Freedon kawai ke wannan kuskure ba, Rediyon Nagarta ma suna yi. Kamata ya yi su dinga cewa SAI KA YI NESA DA REDIYONKA ba KA MATSA KUSA DA REDIYONKA ba. Saboda idan ana shiri kai tsaye kai mai sauraro ka kira waya, in kana kusa da rediyon da kake sauraron shirin ko talabijin za ka ji kuwwa a shirin. Shawarar da masu gabatar da shirin za su ba ka ita ce ka yi nesa da rediyonka ba KA MATSA KUSA DA REDIYONKA ba. Don kana matsawa kusa kuwwar za ta karu ba za a ji me kake fadi a shirin ba. Sai ma’aikatan rediyo da na talabijin da ke gudanar da shirye-shirye kai tsaye da ake kiran waya su kiyaye’
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.