Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, shida ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da shida ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Yau ashirin da shida ga wata, ma’aikata sun ce hantsi fa ya fara duban bakin ludayi. Ya kamata a ce an soma jin dilin-dilin.
 2. Shekara daya da wata hudu ke nan ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, ke ci gaba da dakon ariyas na sabon albashi, har yau ba amo ba labari.
 3. Farashin kayan abinci na ci gaba da tashin gwuron zabi a kasuwa.
 4. Yau take ranar Hausa a duniya bakidaya. Har na tuna shekarar 1988 zuwa 1991 da muka yi karatun digiri na farko a A.B.U. Zariya, mu ‘yan ajinmu mun yi namu yunkurin na farfado da kungiyar habaka Hausa. Shugabannin kungiyar a ajin namu su ne:
  Zubairu Sada, ina jin yana New Nigeria yanzun shi ne shugaba.
  Sai Samaila Mijinyawa malami a KASU a yanzun haka, shi ne mataimakin shugaba.
  Ni ne uban sabga wato Social Director.
  Sai Sani Magaji Kudan da a yanzun jan wuya ne a imigireshan da ke Legas shi ne mataimakina.
  Sai su Musa Abdulkarim tsohon shugaban karamar hukumar Makarfi, da farfesa Balarabe Abdullahi da a yanzun haka ke koyar da Hausa a ABU, da Ciroma Bala da ke koyarwa a wata makaranta da ke nan cikin garin Kaduna. Sai Musa wanda muke ce masa Musa Abu Lullube wanda babban sakatare ne na SUBEB ta nan Kaduna, sai Rabiu Musa Mahuta babban sakatare a ma’aikata yada labaru ta jihar Katsina, da Abdulmumi muna ce masa CARTER da shi ma jan wuya ne a yanzun a imigireshan, akwai Sabo Yakudina daga Bauci, da Kalakala da wata Auta Takobi da wani mutumun Bakori da sunansa ya bace mun yazun yana da uku-uku a baka. Da Mohammed Mamson mutumin Neja. A lokacin muna karkashin jagorancin Malam Adamu Malumfashi da Malam Bello Alhassan, da marigayi Malam Abubakar Kafin Hausa. Har su Musa Dankwairo suka mun waka. Aliyu Kankara da ba a sashenmu yake karatu ba, kuma yana kasa da mu, yakan zo da kalangu yana kida yana cewa shi ne shatan ABU.
 5. Hukumar lafiya ta duniya WHO a takaice, ta ce an yi nasarar fatattakar cutar shan inna wato foliyo, har da ita kanta Innar da ke haddasa cutar daga Nijeriya da Afirka gabadaya. Har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce burinsa ya cika na fatattakar cutar daga Nijeriya, kuma haka yake sa ran fatattakar kwaronabairos daga Nijeriya.
 6. A Nijeriyar zuwa larabar nan akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 252 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Filato 50
Inugu 35
Ribas 27
Legas 26
Abuja 18
Kaduna 18
Ekiti 10
Kano 10
Taraba 9
Anambara 8
Edo 8
Oyo 8
Delta 7
Ogun 6
Abiya 5
Bayelsa 5
Ebonyi 1
Oshun 1

Jimillar da suka harbu 52,800
Jimillar da suka warke 39,964
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1007
Jimillar da ke jinya 11,829

 1. A Tangaza kidinfas sun yi kidinafin amarya da uwa mai shayarwa.
 2. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace, fiye da wata biyar ba wutar lantarki, shekara da shekaru ba hanya, ga tsadar taki suna fama da shi, gadar da sukan samu su haura ta balle, da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkwari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Ga wa’adinsa na shirin karewa ya kasa gyara musu.

Mu wayi gari lafiya.

Af! A rana mai kamar ta yau wato ashirin da shida ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da goma sha bakwai 26/8/2017 na yi wannan rubutu da ke biye:

‘Jama’a barkanmu da asubahin asabar hudu ga watan zulhaj, shekara ta 1438 bayan hijirar cikamakin annabawa, kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da shida ga watan agustan shekarar 2017.
Yau shawara ce ga Gwamnanmu na jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai.
Jiya na ji Kwamishinan ilimi da kimiyya da fasaha na jihar Kaduna Farfesa Andrew Nok, na bayani a wajen wani taro na horas da malaman kimiyya da kere-kere, cewa Gwamnatin jihar Kaduna, nan gaba kadan, za ta tura malaman jiha da ke koyarwa a wannan fannoni da aka fi sani da TECHNICAL EDUCATION kasar Jamus don horas da su a can. Kodayake ban ji ya ambaci yawan malaman ba.
Shawarar tawa ita ce Gwamna ya zo kwalejinmu wato Kaduna Polytechnic, muna da sashen da ake ce masa EDUCATION TECHNICAL, duk wani kayan aikin koyar da wannan fanni muna da su. Gyaran lantarki, mota, gini, kafinta, laturonik, da sauransu. Kuma Daktoci da muke da su a sashen masu yawan gaske a wadannan fannoni a kwalejin Polytechnic ta Kaduna, ba duka Jami’o’in kasar nan ke da irinsu, da kwarewarsu ba. Don ni kaina nan na yi karatun difiloma ta koyon aikin malanta a shekarar 2006. Na san suna da kwararrun malamai fiye da yadda ake zatto.
Gwamna maimakon kwashe ‘yan canjin da muke tattalinsu a jiha don sauke nauyin jama’a musamman hanyoyi, da asibiti, da ilimin, da tsaro, zai fi dacewa a tattala, a turo mana malaman da za a tura Jamus mu horas da su. Ka ga Gwamna ya taimaka wa gida da bunkasar kwalejin, da tsimin kudin, da malaman da za a horas. Na san daukar malami guda a kai shi Jamus ba karamin kudi za a kashe ba. Tunda ana batun mu ci shinkafa ‘yar gida, komai mu koma ga na gida, to makarantun ma, da malaman muna da su a gida.
Amma fa shawara ce.
Mu yini lafiya’

Za a iya leka rubutun na yau a TaskarGuibi da ke DCL Hausa a:

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2685759765029751&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Exit mobile version