Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Jama’a assalama alaikum barkanmu da asubahin lahadi, ashirin ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha biyu ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Yau ma zan soma da batun talaka na ci gaba da biyan kudin zama a duhu. Rabonmu da wuta yau kusan kwana uku, haka muke yini, muke kwana, muke tashi babu wutar. Yanzun haka karfe uku saura kwata na dare nake wannan rubutu a duhu ga sauro na ta gada abinsa. Ga daya nan ma yana kawo mun farmaki.
  2. Ana ci gaba da kwaso ‘yan Nijeriya da ke kasashen waje. Na baya-bayan nan guda ashirin da tara ne daga Labanan, sai wasu daga Maleshiya da kasar Tailan da aka kwaso suke kan hanyarsu ta isowa Nijeriya.
  3. Sojojin Nijeriya na bikin cika shekara dari da hamsin da bakwai da kafuwa. In ba a manta ba ga masu bibiyata na bayyana cewa na rubuta wata makala ta tarihin aikin soja da harshen Hausa, har sashen nazarin harsuna da ilimin harshe na jami’ar jihar Kaduna ya buga a kundin makaloli na bincike na bara KADAURA, kuma bai fi mako biyu da Najib Tsafe ya yi hira da ni a kai, a shirinsa na Hausa Tsantsa a rediyon Libati ba.
  4. Kudaden da ke hannun jama’a suke ma’amala da su yau da kullum, sun ragu a watan jiya na Yuni zuwa naira tiriliyan biyu, da ‘yan kai (2.29trn).
  5. An janye ‘yan sandan da ke yi wa Ibrahim Magu garkuwa da rakiya, an umarci kowanne ya koma wajen aikinsa.
  6. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata uku ke nan suna zaman jiran ariyas na sabon albashi.
  7. Shekaranjiya na je sayan garin masara kwatan buhu, a da ina sayen kwatan naira dubu biyu, ya kai dubu biyu da dari biyar, ya kai dubu uku, ya dade a naira dubu uku da dari biyar, to shekaranjiya naira dubu biyar na sayo shi. Ka ga buhun garin ya zama naira dubu ashirin, rabi naira dubu goma, maimakon buhun da nake saya naira dubu takwas.
  8. Zuwa jiya a duniya bakidaya mutum miliyan goma sha biyu da rabi ya harbu da kwaronabairos, sai mutum dubu dari biyar da sittin da shida, da dari uku da goma da ya riga mu gidan gaskiya.
  9. Jiya kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su dari biyar da saba’in da biyar a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 224
Oyo 85
Abuja 68
Ribas 49
Kaduna 39
Edo 31
Inugu 30
Delta 11
Neja 10
Katsina 9
Ebonyi 5
Gwambe 3
Jigawa 3
Filato 2
Nasarawa 2
Barno 2
Kano 1
Abiya 1

  • Kano 1 Kaduna 39!

Jimilar wadanda suka harbu 31,323
Jimilar wadanda suka warke 12,795
Jimillar wadanda suka riga mu gidan gaskiya 709
Jimillar wadanda ke jinya 17,819

Mu wayi gari lafiya.

Af a rana mai kamar ta yau 12 ga watan Yuli na shekarar 2017 yau shekara uku daidai na yi wannan rubutun da ke biye :

‘Jama’a barkanmu da asubahin laraba goma sha takwas ga watan shawwal shekara ta 1438 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha biyu ga watan yulin shekarar 2017.
Jiya na ji a BBC cewa Mukaddashin Shugaban Kasa Ferfesa Yemi Osinbanjo na kan hanyarsa ta zuwa Landan don ganawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari karo na farko tun bayan tafiyarsa jinya. Bayanai na nuna Shugaban Kasan ne ya umarce shi ya same shi a can.
Tunanina Zaki ne ke shirya yadda zai dawo ya karbe mulki daga hannun kuraye da dila da suka mamaye gindin mulki suna ta gada da tunanin Zaki ya tafi kenan har abada ba zai komo ya karbe gandunsa ba, da ake ta tattaka sauran kananan dabbobi da namun daji.
Aisha Buhari ta tabbatar da Lion na nan komowa don fatattakar Hyenas da Jackals kamar yadda Sanata Shehu Sani ya yi korafi sun mamaye Kingdom na mulkin gandun Nijeriya suna ta mulkin kama karya.
Bangaren fassara na ji shirin kowanne gauta na rediyon firidom a shirin jiya da daddare ya fassara JACKAL da KUREGE. Jackal dila ne ba kurege ba. Allah Ya dawo mana da Zaki gida lafiya mu yi kallon bureden da za a sha tsakaninsa da Kuraye da Dila maciya amana.
Mu yini lafiya’

Hmmmmmmmmm! Bakina da goro.

Hoton da ke biye ga wadanda suke iya ganin hoto a rubutuna, iyayena ne Salihu da Idris ke tambayar yaushe za su koma makaranta ne?

Za a iya leka rubutun labarun nawa na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=494944097974574&id=114506719351649

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply